Rikicin Sarauta: ’Yan Sanda sun yi wa gidan Sarki Kabiru kawanya | Aminiya

Rikicin Sarauta: ’Yan Sanda sun yi wa gidan Sarki Kabiru kawanya

    Abbas Dalibi, Legas

An wayi gari da ganin dandazon ’yan sanda a kofar gidan Sarki Kabiru Garba da ke Ebute Meta a kwaryar Birnin Legas a Lahadi 3 ga Janairu, 2020.

’Yan sandan sun zagaye gidan ne yayin da ake shirin fara gagarumin bikin nadin sarautar Alhaji Ali, da ga Sarki Kabiru, bayan da babban dansa Alhaji Sani Kabiru ya rasu kwana 10 da suka gabata.

A ranar Lahadin ne aka shirya gagarumin bikin nadin  Alhaji Ali Kabiru wanda aka shirya Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da wasu mukkarabansa za su halarta.

Aminiya ta tuntubi Sakataren Majalisar Masarautar Sarki Sani Kabiru, Alhaji Ahmad Danbbata,inda ya tabbatar da  cewa an shirya taro a ranar Lahadin amma suka wayi gari da ganin dandazon ’yan sanda a kofar gidan.

“Yanzu haka da nake magana da kai, Mashawarcin Gwamnan Jihar Legas ya riga ya iso domin sharen fage kafin zuwan gwamnan, amma ya yi mamakin yadda Rundunar ’Yan Sanda ta hana taron.

“Muna ganin an hana taron ne saboda dalilai na hana taruwar jama’a domin kare yaduwar cutar COVID-19.

“Mun yi taron sadakar uku na marigayin a ranar Lahadin makon jiya, a lokacin ne mu kayi nadin sabon sarki, Alhaji Aliyu Kabiru Garba

“Iyalan gidan sarki tare da malamai sun yi taron sadakar 7 a ranar Alhamis 31 ga watan Disamban 2020, mu kuma ’yan Majalisar Sarki mun shirya namu taron ne a ranar Lahadi saboda muna sa ran Gwamnan Legas da sauran manyyan baki za su halarta.

“Amma tun da abun ya zo da haka, tuni muka ba da sanarwar dage taron domin mu masu bin doka ne, amma nadin Sarki mun riga mun yi,” inji shi.

Yace kara da cewa akwai daurin auren kannen marigayin mata da aka shirya yi bayan addu’ar 7 amma tun da lamarin yazo da haka an daga sai zuwa nan gaba.

Rikicin Sarauta

Kurar rikicin sarautar ta sake kunno kai ne a Jihar Legas tun bayan rasuwar Sarki Sani Kabiru bayan da danginsa da ’Yan Majalisarsa suka nada kaninsa Alhaji Ali Kabiru a matsayin sarkin Hausawan Legas.

Lamarin ya sa Masarautar Sarki Dogara ta ce afafau ba za ta sabu ba, domin akwai sarkin Hausawa a Legas, wato Alhaji Aminu Idris Yaro,  don haka babu dalilin da zai sa wasu su nada wani sarki, su raba kan al’umma.

Masarautar ta kuma ce za ta bi duk hanyoyin da suka dace domin ganin ta hana yunkurin nada wani sabon Sarkin Hausawan Legas.

Wakilin Aminiya ya tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, SP Muyiwa Adejobi domin samun karin bayani.

Sai dai ya shaida wa wakilin namu kawo yanzu ba shi da masaniya a kan kawanyar da ake zargin jami’an Rundunar sun yi a gidan Sarkin, amma ya kara da cewa zai yi bincike sannan ya yi karin bayani.