✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Tigray: An janye dokar ta-baci a Habasha

Majalisar ta sanar da danye dokar ce a ranar Talata, sabanin watan Mayu da aka ayyan dokar da farko.

Gwamnatin kasar Habasha ta janye dokar ta-baci na wata shida da ta sanya a lokacin da mayakan Tigray suka yi barazanar shiga Addis Ababa, fadar gwamnatin kasar, da yaki.

Majalisar dokokin ta amince da janye dokar ce bayan Fira Minista Abiy Ahmed ya gabatar mata da bukatar yin hakan a watan Janairu.

“Majalisar Dokokin Habasha ta amince da janye dokar ta-baci da aka ayyana na tsawon wata shida,” kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.

Majalisar ta sanar da danye dokar ce a ranar Talata, sabanin wa’adin watan Mayu da aka sanya wa dokar da farko.

A ranar 2 ga watan Nuwamba ne aka sanya dokar bayan mayakan Tigray sun kwace wasu garuruwa masu tazarar kilomita 400 daga birnin Addis Ababa.

Bayan kafa dokar, gwamnatin kasar ta rika tsare ’yan Tigray da ke birnin Addis Ababa da sauran wurare, wanda ya jawo mata suka daga kungoyin kare hakkin Adam, musamman Amnesty International.

Janye dokar na zuwa ne bayan gwamnatin kasar Habasha ta fara kai hare-hare da jirage marasa matuka tana kora mayakan na Tigray zuwa yankinsu tun a watan Dismaba.

Gwamnatin dai ta ce ba za ta bi su zuwa cikin yankinsu ba, amma wasu mazauna yankin sun ce jiragen sun kai wasu hare-hare a yankin.

A watan Janairu ne mayakan Tigray suka kaddamar da hare-hare a yankin Afar, a matsayin ramuwar gayya ga dakarun gwamnati, wanda ke haifar da fargaba game da yiwuwar tsagaita wuta a tsakanin bangarorin.

Rikicin ya lakume dubban rayuwa wasu kuma sun yi kaura daga gidajensu baya ga wadanda ke fusktantar barazanar matsananciyar yunwa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.