✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine: An ja kunnen ’yan Najeriya mazauna kasar

Ofishin Jakadancin Najeriya ya gargadi ’yan kasar game da yin tafiye-tafiye barkatai.

Ofishin Jakadancin Najeriya a kasar Ukraine ya gargadi ’yan Najeriya mazauna kasar da su kiyayi yin tafiye-tafiye barkatai da kuma shiga yankunan da ke fama da rikici a kasar.

A shekarar da ta wuce, Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya a Ukraine, Martin Dele Lawani, ya bayyana cewa ’yan Najeriya akalla 8,000 ne suke karatu da kuma kasuwancinsu a Ukraine.

Kwanaki uku suka wuce, Birtaniya ta ba da umarnin janye ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke kasar kan fargabar yiwuwar hari daga kasar Rasha a kowane lokaci.

Wata sanarwa da aka fitar ga ’yan Najeriyar ta ce, “Ana jan hankalin ’yan Najeriya da cewa duk inda za su je su kasance dauke da katin shaidarsu.

“Ana kuma shawartar ’yan Najeriya mazauna Ukraine da su tuntubi Ofishin Jakadancin Najeriya game da karin bayani kan halin da ake ciki a kasar nan game da sha’anin tsaro.”