✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine: Farashin danyen mai ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 14

Wannan dai shi ne farashi mafi armashi da man ya taba kai wa tun 2008.

Yayin da rikicin Rasha da Ukraine yake dada ta’azzara, da alama kakar Najeriya da ta sauran kasashe masu arzikin man fetur ta yanke saka, yayin da farashin gangar danyen mai ya doshi Dalar Amurka 140 a kasuwannin duniya.

Wannan dai shi ne farashi mafi armashi da man ya taba kai wa tun shekara ta 2008.

Hakan dai na zuwa ne yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kakaba wa Rasha takunkumi saboda ci gaba da mamayar da take yi wa Ukraine.

Farashin man dai ya tashi da sama da $10 a kan kowace ganga a ranar Litinin.

Tashin farashin dai ya biyo bayan gargadin da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya yi cewa Ukraine na dab da wargajewa bayan da dakarun kasarsa suka ci gaba da yin luguden wuta a kan muhimman wurare na kasar.

A cikin karshen mako dai wani yunkurin tsagaita wuta na wucin gadi ya ci tura, yayin da bangarori biyun ke ci gaba da nuna wa juna yatsa.

Kamfanin mai na kasar Libya ya ce farashin ya dada karuwa ne bayan wasu masu dauke da makamai suka rufe wasu rijiyoyin mai guda biyu, lamarin da ya sa ala tilas kasar ta gaza samar da adadin da aka ware mata da ganga 330,000 a kullum.

Ya zuwa safiyar Litinin din dai, farashin ya karu da kimanin $10 a kasuwar birnin Tokyo ta Japan, inda ya kai kusan $124.74 kan kowacce ganga.

Rabon dai da a samu irin wannan karin farashin tun a 2008, lokacin da man Amurka ya kai $145.29.