✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin ’Yan Acaba Da ’Yan Sanda Ya Janyo Asarar Rai A Legas

Wani mahayin babur da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya rasa ransa sakamakon wata hatsaniya da ta barke tsakanin ’yan acaba da ’yan…

Wani mahayin babur da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya rasa ransa sakamakon wata hatsaniya da ta barke tsakanin ’yan acaba da ’yan sanda a Legas.

Hayaniyar dai ta fara ne bayan wata mota ta bige wani dan acaba a gadar Abuke-Egba da misalin karfe 4:30 na yamma.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya ce faruwar hakan ke da wuya ’yan acabar suka tada hayaniya a wurin.

Ya ce ganin haka ya sanya ’yan sanda suka je wurin domin kwantar da tarzomar, sai dai abin bai yi wa ’yan acabar dadi ba.

Take suka rufar wa ’yan sandan da duka a cewarsa.

“Muna sane da abin da ya faru a unguwar Oka-Oba ta Legas.

“Kuma mummunan lamarin ya yi sandiyar mutuwar mutum guda.

“Sai dai yanzu komai ya daidaita, domin jami’anmu na wajen don tabbatar da ci gaba da bin doka da oda”, in ji kakakin.