✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rishi Sunak: Fira Minista mafi karancin shekaru a Birtaniya

Duk abin da ya kamata Ku sani kan Rishi Sunak, wanda shi ne Fira Minista mafi karancin shekaru a tsawon shekara 200 a Birtaniya

A safiyar Talata 25 ga Oktoba, 2022  Fira Minista mafi karancin shekaru a tarihin kasar Birtaniya na sama da shekara 200, Rishi Sunak, zai karbi rantsuwar fara aiki.

Matashin mai shekara 42 zai fara aiki ne bayan ganawa da Sarki Charles III, wanda zai rantsar da shi kafin karfe 12 na rana.

Hakan zai kasance ne bayan Fira Minista Mai Barin Gado, Liz Truss ta jagoranci zamanta na karshe da Majalisar Ministocin kasar, inda daga nan za ta je ta ganawar karshe da Sarki Charles III a Fadar Buckingham.

Tun bayan samun nasarsa ta zama sabon Shugaban na Jam’iyyar Conservative a ranar Litinin, Sunak bayyana cewa zai karbi shugabanci ne a lokacin da Birtaniya ke cikin babbar matsalar tattalin arziki da neman daidaituwar al’amura.

Matsalolin da kasar ke ciki sun sa jam’iyyun adawa — Scottish National Party, the Liberal Democrats, da  Green Party — kira da a gaggauta yin babban zabe.

Sai dai matashin, kuma hamshakin attajiri, ya bayyana cewa babu maganar gaggawar yin zabe, babban abin da ke gaban Jam’iyyar Conservative shi ne hada kan kasar.

Takaitaccen tarihin Rishi Sunak

Rishi Sunak wanda iyayensa baki ne ’yan kasar Indiya, shi ne mutum na farko dan asalin nahiyar Asiya da zai zama Fira Ministan Birtaniya.

Iyayensa ma’aikatan lafiya ne kuma sun haife shi ne a 1980 a Southampton bayan sun koma Birtaniya daga yankin Gabashin Afirka.

Zai kuma karbi ragamar kasar ce  bayan samu rinjaye a zaben Shugaban Jam’iyyar Conservative ta masu ra’ayin rikau, daga hannun Liz Truss, mace ta farko da ta taba zama Fira Ministan Birtaniya.

Rishi Sunak, ya karanci fannin Siyasa, Falsafa da Tattalin Arziki a Jami’ar Oxford.

Kwararren Jami’in Banki ne kuma Masanin Harkokin zuba Jari da Gudanar da Kudade.

Shi da matarsa, Akshata Murthy, su ne na 122 a jerin mutane mafiya arziki a Birtaniya kuma dukiyarsu ta kai Fam miliyan 730.

A shekarar 2015 aka fara zabensa a matsayin dan Majalisar Dokoki mai Wakiltar Richmon, a Arewacin Yorkshire.

Matashin, ya kasance Sakataren Kula da Kudaden Tallafin COVID-19 (2019-2020), lokacin tsohon Fira Minista, Boris Johnson.

Daga baya ya zama Ministan Kudi daga 2020 zuwa 2022.

Matarsa, Akshata Murthy, ’yar hamshakin attajirin kasar Indiya Narayana Murthy ce.

’Ya’yansa uku kuma mabiyan addinin Hindu ne.

A yanzu zai jagoranci kasar ne bayan Liz Truss ta yi murabus daga matsayinta bayan kwana 45 da rantsar da ita.

Hakan ne ya mayar da ita Fira Minista da mulkinta ya fi kowanne gajarta a tarihin kasar.

Misis Truss ta yi murabus ne saboda gazawarta wajen shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.

Mai barin gadon ta karbi mulki ne a ranar 6 ga Satumba bayan saukar Boris Johnson wanda rikice-rikicen da suka dabaibaye gwamnatinsa sun sa ’yan Jam’iyyar Conservative a Majalisar Dokokin kasar juya masa baya.

Boris Johnson ya shafe shekara uku a kan mulki mai cike da rudani — kama daga dambarwar neman ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai (Brexit) zuwa zargin sa da take dokoki, da kuma fadi-tashin tattalin arzikin kasar.