✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rochas ya bukaci a zurfafa bincike kan kisan Gulak

Rochas ya ce yana da kyau a zurfafa bincike don gano wadanda suka kashe Gulak.

Tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya bukaci a yi bincike mai zurfi kan kisan Ahmed Gulak, tsohon Mashawarcin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan Harkokin Siyasa da aka yi a jihar.

Rochas wanda shi ne Sanata mai wakiltar Yammancin Imo ya jaddada muhimmancin a yi bincike na tsanaki a gano hakikanin masa hannu wajen salwantar da rayuwar tsohon Shugaban na Jam’iyyar PDP na Kasa.

Ya yi tir da kisan da kuma yadda ya ce zubar da jini ke neman zama ruwan dare a wasu sassa na Najeriya ciki har da jihar ta Imo.

A sakon ta’aziyyarsa ta rasuwar Gulak,  Okorocha ta bakin kakakinsa, Sam Onwhemeodo, ya bayyana jimami tare da fargabar yadda siyasa ta sauya al’amura wadda har ta yi sanadin mutuwar Gulak, da ma wasu manyan mutane.

Ya roki shugabanni da masu fada a ji a Najeriya da su rika taka-tsantsan a kalaman da suke furtawa, don gudun jefa kasar cikin tsaka mai wuya, musamman a yanzu da ake fama da matsalar tsaro.