✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ronaldo ya dawo atisaye bayan jan kunnensa da United ta yi

A makon da ya gabata ne kocin ya nemi ya koma atisaye shi kadai.

Dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da sauran abokan wasansa na kungiyar.

Ronaldo ya dawo cikin tawagar kungiyar ce bayan hukuncin da mai horar da su Erik ten Hag ya dauka a kansa.

A makon da ya gabata ne kocin ya nemi ya koma atisaye shi kadai, a wani bangare na jan kunnen da aka yi masa.

Ronaldo mai shekara 37, ya ki shiga wasan da United da ta buga da Tottenham a ranar Larabar da ta gabata saboda an ajiye shi a benci.

Saboda haka ne Ten Hag ya ki amfani da shi a wasan da Manchester United ta yi 1-1 da Chelsea domin a ladabtar da shi.

Ten Hag ya ce bayan wannan hukunci ba wanda za a kara yi masa.

An gano cewa Ronaldo da Ten Hag sun tattauna a wannan Talatar.

Wasu rahotanni na cewa, akwai yiwuwar dan wasan ya koma Chelsea da taka leda da zarar an bude kasuwar musayar ’yan kwallo a watan Janairu.