✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya jefa kwallo a Gasar Kofin Duniya 5 daban-daban

Ronaldo dai ana masa kallon babbar barazana ga sauran kasashen da ke rukuni guda da Portugal.

Cristiano Ronaldo ya zama mutum na farko da ya jefa kwallo a Gasar Kofin Duniya biyar daban-daban a tarihi.

Ronaldo ya kafa tarihin ne a ranar Alhamis bayan da ya zura kwallon farko a bugun fenareti a wasan da Portugal ta doke Ghana da ci 3-2.

Dan wasan mai shekaru 37 ya kafa tarihin ne a minti na 65 da fara wasan a filin wasa na 974 da ke Doha, inda ya tura tawagar Fernando Santos zuwa mataki na farko a rukunin H da maki biyu tsakaninta da Uruguay da Koriya ta Kudu.

Ronaldo ya shafe tarihin da Pele da Uwe Seeler da Miroslav Klose, suka kafa a Gasar Kofin Duniya.

A makon nan ne Manchester United ta raba gari da Ronaldo bayan ya soki kungiyar da kocinta Erik ten Hag a wata hira da yayi da fitaccen dan jarida, Piers Morgan.

Hankula dai sun karkata kan Ronaldo, kan ko zai iya kafa wannan tarihi, kuma dan wasan ya samu damar hakan cikin minti na goma da take wasa.

To sai dai alkalin wasa ya soke kwallon, amma daga bisani ya samu wannan dama a bugun daga kai sai mai tsaro gida.

Ronaldo dai ana masa kallon babbar barazana ga sauran kasashen da ke rukuni guda da Portugal.