✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya yi fice a harkar kwallon kafa —Messi

Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya yi furuci kan babban abokin hamayyarsa a harkar tamola, Cristiano Ronaldo, inda ya bayyana Ronaldo a…

Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya yi furuci kan babban abokin hamayyarsa a harkar tamola, Cristiano Ronaldo, inda ya bayyana Ronaldo a cikin jerin taurarin ’yan wasa na duniya da suka yi fice a fagen sana’o’insu.

Messi wanda ko shakka babu tauraruwarsa ta fi ta kowane dan wasan na baya da na yanzu haske a kungiyar Barcelona, ya yi abin da masu iya magana kan ce yabon gwani ya zama dole, inda ya ce Cristiano Ronaldo zakaran gwajin dafi ne wanda ya yi fice a harkar kwallon kafa.

Sallamawar da Messi ya yi na zuwa ne bayan da Cristiano Ronaldo ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Karni a ranar Lahadi.

Ronaldo wanda a yanzu hake yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus, shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowanne bajinta daga shekarar 2001 zuwa 2020 yayin bikin ba da lambar yabo ta Globe Soccer Awards da aka gudanar ranar Lahadi a Otal din Armani da ke birnin Dubai.

Sai dai a yayin da muhawara ba za ta yanke ba a tsakanin masoya kwallon kafa dangane da ayar tambaya ta wane dan wasa ne mafi kyawu kuma sha-gaba a tsakanin Messi da Ronaldo, Messi wanda ya fito daga kasar Argentina ya sallama da kansa dangane da irin girmamawarsa ga dan wasan na Juventus dan kasar Portugal.

A bisa madogarar ’yan Hausa ta ‘idan ana dara fidda uwa ake’, Messi ya yi ammana da cewa Ronaldo gwani ne wanda ya yi fice da kuma fintinkau tamkar wasu ’yan tsirarun taurari da suka zama sha-kundum a harkokin da suka sa gaba irinsu Rafael Nadal da Roger Federer, ’yan wasan kwallon tennis, sai kuma LeBron James dan wasan kwallon kwando.

“Akwai ’yan wasa da dama da suka kasance masu ban sha’awa da kayatarwa, kuma a dukkan wasanni na duniya a kodayaushe ana samun wanda ya yi fice kuma dole a yaba masa.

“Cristiano ya yi fice a harkar kwallon kafa, kuma akwai taurarin ’yan wasa da dole ne a yaba masu saboda yadda suke jajircewa da ba da himma ta gaske,” a cewar Messi yayin zantawa da jaridar La Sexta ta kasar Andalus.