Ronaldo zai gana da sabon kocin Manchester United | Aminiya

Ronaldo zai gana da sabon kocin Manchester United

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo
    Abubakar Maccido Maradun

Cristiano Ronaldo ya dawo Old Trafford domin ganawa da sabon mai horas da ‘yan wasan Manchester United, Erik ten Hag.

Ana sa ran tattaunawar tasu za ta kasance a kan makomar dan wasan a kungiyar.

A baya dai dan wasan mai shekara 37, ya nuna wa United din bukatar son barin kungiyar gabanin fara kakar wasannin bana.

Wasu suna ganin wannan ba ya rasa nasaba da rashin yin abun a zo a gani da kungiyar ta yi a kakar wasannin bara, wadda ta haifar musu kasa samun gurbi a wasannin gasar Zakarun Turai ta bana.

Sai dai duk da wannan yunkurin na Ronaldo, har yanzu bai samu wata kungiya da ta nuna ra’ayin daukar dan wasan gaban na Man United din ba.