✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo zai rattaba hannu da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya a farkon watan Janairu

Ana sa ran kungiyar ta saye shi a kan Yuro miliyan 173

Tsohon dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo zai rattaba hannu da kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke kasar Saudiyya ranar daya ga watan Janairun 2023.

Rahotanni sun ce dan wasan dan asalin kasar Portugal, zai koma Al-Nassr a kan Yuro miliyan 173, bayan ficewarsa daga Manchester mai cike da ce-ce-ku-ce, ana saura kwana biyu a fara Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Qatar.

Hakan dai zai sa dan wasan ya kafa tarihin da ba a taba kafa irinsa ba a duniyar kwallon kafa na dan wasan da aka taba saye da kudi masu yawa.

Kafar yada labarai ta MARCA ta rawaito cewa dan wasan zai rattaba hannun ne a watan Janairun, kuma cinikin farko zai fara ne a kan kudi Yuro miliyan 86 lakadan, yayin da ragowar kuma za su zo ne a tallace-tallace.

Dan wasan ya rasa kulob ne a karshen watan da ya gabata bayan wata takaddamar da ta barke tsakaninsa da United biyo bayan wata tattanawa da yi ta gidan talabijin da Piers Morgan.

Al-Nassr dai na daya daga cikin kungiyoyi mafi shahara a Saudiyya, kasancewar ta taba lashe gasar babbar gasar kasar har sau tara, inda ko a 2019 ita ce ta lashe gasar.

Ko a shekarun 2020 da kuma 2021 ma kiris ya rage kungiyar ta lashe gasar, amma dai duk da haka ta lashe kofin Super Cup na kasar.