✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufaida Umar ce gwarzuwar gasar Aminiya-Trust

Labarin Dimokuradiyyar Talaka ya yi zarra a gasar Aminiya-Trust ta 2020.

Alkalan gasar rubutun kagaggun gajerun labarai ta Aminiya-Trust ta 2020, sun bayyana Rufaida Umar Ibrahim a matsayin wacce ta lashe gasar.

Labarin da ta rubuta mai suna Dimokuradiyyar Talaka ne ya yi zarra a cikin labarai da marubuta kimanin dari da suka fafata a gasar.

An sanar da nasararta ce a bikin karrama zakaru uku da labaran da suka rubuta suka yi zarra a gasar, a daren ranar Asabar 5 ga Yuni, 2021 a Kaduna.

Dimokuradiyyar Talaka, labari ne “game da wani matashi mai suna Rabi’u, wanda ya tsoma kansa cikin harkar siyasa. Sai dai a karshe lamura suka juye, sabanin tunaninsa; wanda ya yi silar rusa dukkan mafarkansa.”

Wanda ya zo a matsayi na biyu a gasar shi ne Mubarak Idris Abubakar wanda ya rubuta labarin Tufka da Warwara.

Tufka da Warwara, labarin wani Gwamna ne da ya kammala wa’adin mulkinsa amma yana kyashin ya mataimakinsa ya gaji kujerar; duk kuwa da cewa mutane na son sa.

“Sai gwamnan ya yi amfani da tuggu da lissafi irin na siyasa, ya kifar da mataimakin nasa; ya dora wanda yake ganin zai ba shi damar cimma burinsa.

“Sai dai hakan ya faskara, inda labari ya sha bamban,” kamar yadda Marubucin ya bayyana a kunshiyar labarin.

Labarin da Ubaida Usman ta rubuta, na suna Ranar kin dillanci, shi ne ya zo na uku a gasar.

A lokacin bikin an kuma kaddamar da littafi da ke dauke da labaran da karin wasu 12 da suke bi musu baya wajen taka muhimmiyar rawa.

Sunan littafin Dambarwar Siyasa: Gajerun Labaran Gasar Aminiya-Trust 2020.