Rufe Jami’o’i: Gwamnati Ba Ta So Ta Yi Wa ASUU Karya —Abdullahi Adamu | Aminiya

Rufe Jami’o’i: Gwamnati Ba Ta So Ta Yi Wa ASUU Karya —Abdullahi Adamu

    Sagir Saleh Kano da Abba Adamu Musa

Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce matsayar da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta dauka abu ne da zai yi wuya a daidaita a kai.

Ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da Aminiya a Abuja, inda ya ce gwamnati ba ta so ta yi wa malaman jami’a karya ne, don haka take lalubo wasu hanyoyin sasantawa da kungiyarsu.