✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rufe shagunan ’yan Najeriya a Ghana tsana ce’

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattijai, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya ce rufe shagunan wasu ’yan Najeriya da Ghana ta yi abin takaici ne. Ghana ta…

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattijai, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya ce rufe shagunan wasu ’yan Najeriya da Ghana ta yi abin takaici ne.

Ghana ta rufe shagunan ne a birnin Accra, matakin da ya harzuka Najeriya har ta yi wa jakadunta da ke can kiranye tare da barazanar kai karar Ghana a gaban kotun ECOWAS, muddin ta gano karya dokar shige da fice ta yankin Yammacin Afirka.

A sanarwa da kakakinsa, Uchenna Awom ya fitar, Sanata Abariba ya ce abin da Ghana ke yi wa baki musamman ‘yan Najeriya nau’i ne na kin jinin baki.

Ya ce, “Ya kamata Ghana su wanke kansu daga wadannan zarge-zargen ta hanyar dakatar da kulle shagunan.

“Matakin da suka dauka na cewa ’yan kasar ne kadai ke da ikon sayar da kaya dai-daya ya saba yarjejeniyoyin ECOWAS na zaman tare.

“Ina amfanin yarjejeniyar da aka yi idan kowacce kasa za ta yi dokoki masu cin karo da ita? Hakika wannan ya saba da makasudin kirkirar ECOWAS”, inji Sanata Abaribe.

Shugaban marasa rinjayen ya bukaci ECOWAS da ta yi wa tufkar hanci ta hanyar daukar matakin da ya dace domin magance kalubalen da kasuwanci ba tare da shinge ba ke fuskanta a yankin.