Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba | Aminiya

Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba

    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao da Bilkisu Ahmed

Domin sauke shirin latsa nan

A kwana akalla 220 da gwamnatin Najeriya ta rufe harkokin kafar sada zumunta ta Twitter, ’yan kasar sun tafka asarar makudan kudade, a yayin da gwamantin kuma ta ci gagarumar riba a sakamakon matakin da ta dauka.

Masana sun yi bayanin irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta rika samu daga harajin da za ta rika karba daga hannun kamfanin Twitter a sakamakon amfanin da ’yan Najeriya suke yi da kafarsa, domin gudanar da harokinsu na kasuwanci da kuma sadar da zumunta.