✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruftawar gada ta yi ajalin mutum 132 a Indiya

An bude gadar ce ba tare da samun takardar inganci daga hukumomin da ke kula da aikin ba.

Akalla mutane 132 sun mutu lokacin da wata gadar da ta kwashe shekaru sama da 100 ana amfani da ita ta rushe a Jihar Gujerat da ke Kasar Indiya.

Ministan da ke kula da yankin, Harsh Sanghavi ne ya shaida wa manema labarai hakan a safiyar Litinin din nan.

Sanghavi ya ce adadin wadanda suka mutun ya karu ne daga alkaluman mutum 68 da aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Lahadi, inda har yanzu ana ci gaba da aikin ceto.

Kafin wannan sanarwa, Ministan da ke kula da Yammacin jihar, Brijesh Merja ya tabbatar da mutuwar mutanen 60 sakamakon hadarin, yayin da ya ce kuma an yi nasarar ceto mutane sama da 80 da ransu ciki har da wadanda suka fada ruwa.

Hukumomin sun ce akalla mutane kusan 500 ke kan gadar lokacin da ta rufta sakamakon sakewar da robobin da ke rike da ita suka yi, cikin su har da mata da yara.

Ita dai wannan gadar ba’a dade da kammala gyaranta ba, kuma tana garin Morbi ne da ke da nisan kilomita 200 daga Ahmedabad a Jihar Yammacin Gujerat.

Kafofin yada labaran kasar sun ce mutanen da suka taru akan gadar suna gudanar da ibada ne akan kogin Machchhu.

Haka kuma wasu kafofi sun nuna hotunan bidiyon da ake bayyana cewar na hadarin ne dauke da mutanen da ke kokarin yin fito domin tsira da rayukansu.

Kamfanin talabijin na NDTV ya ce an bude gadar ce ba tare da samun takardar inganci daga hukumomin da ke kula da aikin ba.

Firaminista Narendra Modi, ya sanar cewa za a bai wa kowanne daga iyalan mamatan diyyar Rupees 200,000 (Dala 2,428) yayin da kuma wadanda suka jikkata za su samu Rupees 50,000 (dala 607).