✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ruftawar kasa ta kashe masu hakar ma’adanai biyu a Kogi

Har an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Mutum biyu ne suka rasa rayukansu a wurin hakar ma’adanai na Ika-Ogboyaga da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi bayan wani bangare na ginin kasa ya rufta kansu.

Aminiya ta samu rahotan cewa, lamarin ya faru ne a karshen mako, inda wasu matasa biyu – Attah da Amodu suka mutu.

Wani ganau ya ce, mutanen yankin da suka kai dauki wurin da lamarin ya faru, tuni sun kwashe gawarwakin wadanda karar kwanan ta cim masu kuma har an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Mataimakin Kwamandan Rundunar Sibil Difens kuma Shugaban Ma’adanai na jihar, Nkom Samson Katung wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’ansu sun fara gudanar da bincike domin gano mamallakin wurin da ya rufta.

Ya kara da cewa, an umurci jami’an da su hada kai da Sarakunan gargajiya domin dakatar da ayyukan da suka saba wa doka a yankin.