✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ‘Operation Hadin Kai’ ta kashe mayakan ISWAP 23 a Borno

Sojoji sun yi mayakan kofar rago a kauyen Komala da ya yi iyaka da Dajin Sambisa.

Dakarun Sojin Kasa na Najeriya sun yi nasarar kashe mayakan ISWAP 23 a Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka kashe ’yan ta’addan a wani harin kwantan bauna da suka kai a ranar 23 ga watan Janairun 2023 a kusa da wani barikin sojoji da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’addan bayan da suka kaddamar da harin kwantan bauna a kauyen Komala da ya yi iyaka da Dajin Sambisa.

A cewarsa, an yi wa maharan kofar rago yayin da suka kai wa sojojin farmaki a cikin jerin gwanon motoci kirar Hilux,  (MRAP) da kuma babura.

Kazalika, ya ce an samu nasarar kashe mayakan tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama wadda dakarunta suka yi musu ruwan wuta daga sama.

Ya ce sojojin sun kuma kwato wata motar yaki mai dakon bindiga mai suna MRA da kuma babura uku daga hannun ‘yan ta’addan.

Ya kuma bayyana cewa a ranar 13 ga watan Junairun shekarar 2023 sojojin sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata wata mota kirar MRAP a lokacin da suka kai wa sojojin hari a kan titin Damboa zuwa Azir.