Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sanar da bude shafinta ga masu sha’awar neman gurbin shiga aikin na 2021 a matakin kurtu wato ‘Airmen’ da ‘Airwomen’.
Sanarwar da ta fitar ta ce za a bude shafin daga ranar 2 zuwa 30 ga watan Maris na 2021, inda za a tantance wadanda suka nemi aikin daga ranar 17 ga watan Mayu zuwa 12 ga Yulin 2021.
Haka kuma sanarwar da Rundunar ta fitar a shafinta na intanet ta ce rajistar kyauta ce don babu bukatar biyan wani kudi saboda haka a kiyaye da masu damfara.
Su waye suka cancanta su nema?
Dole mai sha’awar shiga aikin ya cika wadannan sharuddan:
- Ya kasance dan asalin Najeriya wanda aka haifa a cikinta.
- Tsawonsa ya kai mita 1.66 ga maza, 1.63 ga mata.
- Ya/ta kasance mai cikakkiyar lafiya.
- Ya/ta kasance wata kotu ba ta taba kama shi da laifi ba.
- Ga rukunin masu shaidar kammala Sakandire, dole ne ya/ta kasance ’yan tsakanin shekara 18 zuwa 22 daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun 2021.
- Ya/ta mallaki takardar shaidar haihuwa ta ainihi wacce Hukumar Kidaya ta Kasa, asibiti ko Karamar Hukuma suka amince da ita ko kuma takardar bayyana shekaru.
- Ya/ta samu ‘Credit’ biyar ciki har da Darasin Lissafi da Turanci a daya daga cikin zama biyu na jarrabawar kammala karatun sakandire ta WAEC/NECO/GCE/NABTEB.
- Ga rukunin masu neman aikin da shaidar sana’o’in hannu, dole ne ya/ta kasance mai shekaru 18 zuwa 25.
- Ya/ta mallaki samu ‘Credit’ a shaidar kammala karatun ‘ND’ ko ‘NCE’ tare da ‘Pass’ biyu da ‘Credit’ a English a zama biyu na zana jarrabawar kammala sakandire ta WAEC/NECO/GCE/NABTEB.
- Kada ya/ta kasance mai dauke da zane ko kowane irin nau’in rubutu a jikinsa kuma ba ya cikin kowace irin kungiyar matsafa ko ta asiri.
Za ku iya samun karin bayani a nan