✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rushe Makarantun Kwana Ya Jawo Rarrabuwar kai a Kenya

Al’ummar Kenya suna ce-ce-ku-ken kan rushe tsarin makarantun kwana na firamare da sakandare da gwamnatin kasar ke shirin yi. Wata mata mai suna Miss Karu…

Al’ummar Kenya suna ce-ce-ku-ken kan rushe tsarin makarantun kwana na firamare da sakandare da gwamnatin kasar ke shirin yi.

Wata mata mai suna Miss Karu ta ce shaida wa manema labarai cewa sam ba ta goyon bayan matakin, musamman lura da iyayen da ma’aikata ne da aka tura wani gari.

Ta ce, “Yaya za su yi da nasu ’ya’yan idan sun tafi aiki? Makota za su bar wa, ko ajiye aikin za su yi su dawo kula da su?”

Shi kuma wani, Paschal A. Nobert, ya ce ba hurumin gwamnati ba ne ta zaba wa iyaye irin makarantar da suke ra’ayin sanya ’ya’yansu.

“Misali mu da ke kauye ba mu da makaranatar je-ka-ka-dawo a kusa da mu sai an yi tafiya mai tsawo soai. Ka ga mu ai sai dai mu hakura da ilimin,” in ji shi.

Sai dai wani mai suna Nathan Mutua ya ce alfanun da ke tattare da sabon tsarin ya fi rashinsa yawa ga mai hankali.

“Iyaye yanzu gudun sauke hakkin da ya rataya a wuyansu suke yi, shi ya sa ’ya’yan duk suka lalace, don haka ina goyon baya,” a cewarsa.

Shi ma wani Ferederick Owoko ce ya yi: “Hakan na da kyau matukar gwamnati za ta maida hanakali wajen inganta ilimin makarantu.”

Za Mu Rage Kudin Makaranta Idan Dokar Ta Fara Aiki  —Gwamnati

Shugaban Sashen Kula da Ilimin Matakin Farko na kasar, Dokta Belio Kipsan, ya ce tsarin zai fara aiki ne a 2023, domin ba wa iyaye damar sanya ido da kula da tarbiyyar ’ya’yansu.

Ya ce domin karfafa wa al’ummar kasar guiwa kan amincewa da tsarin, gwamnati za ta rage musu kudin makarantar da zarar dokar ta fara aiki.

Ya ce, “Muna farin cikin sanr da al’umma cewa kuma wannan tsarin ba wai a iya makarantun gwamnati ya tsaya ba, har da masu zaman kansu.”