✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rushewar gini ta yi ajalin wani a Kano

Rushewar ginin ya yi sanadin jikkata wasu mutane

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Kano, sun bayyana cewa wani mutum ya rsau sakamakon rushewar wani bene mai hawa uku a kan titin Unity da ke jihar.

Wani mutum daya kuma ya samu mummunan rauni sakamakon rutsawa da shi da lamarin ya yi.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 12:40 na rana, lokacin da ma’aikatan da ke wurin suke tsaka da aiki.

Aminiya ta zanta da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da cewa suna aikin ceto mutanen da abun ya rutsa da su, wanda ya ce daya ya mutu, an kuma ceto daya wanda aka garzaya da shi asibiti cikin mummunan yanayi.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 12:40 na rana kuma da isarmu, jami’anmu sun yi nasarar ciro mutum biyu, daya ya mutu, daya kuma an kai shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin kula da lafiyarsa.

“Kayan aikin ginin da aka yi amfani da su ba su dace da yanayin ginin da ake yi ba,” inji shi.

Aminiya ta lura cewa an yi ginin ne a tsakanin wani kankanin wuri.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tantance adadin mutanen da suka rasu ba.