✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan Mariri ya ci matasa biyu a Kano

Matasa biyu sun rasu a ruwan Mariri Ramin Kalanzir a Jihar Kano.

Matasa biyu sun rasu a ruwan Mariri Ramin Kalanzir, Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Mamatan da suka hada da Umar Auwalu mai shekara 15 da kuma Muhammed Nafis, me shekara 20 a duniya, sun rasu ne a ranar Juma’a. 

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da aka raba wa manema labarai a ranar Juma’a.

Abdullahi ya ce hukumar ta samu labarin faruwar lamarin da misalin 07:57 na safe ta bakin wani mai suna Mustapha Musa, nan take kuma ta aike da jami’anta wurin da abun ya faru don kai dauki da misalin karfe 08:10 na safe.

“An fito da su daga ruwan a mace, nan take kuma muka mika su ga mai unguwar Sheka Gabas, Alhaji Umar Yunusa,” A cewar Abdullahi.

Ya ce, har yanzu ba su tabbatar da musabbabin rasuwar yaran ba amma ana kan ci gaba da gudanar da bincike.

Abdullahi, ya shawarci iyaye da su rika hana ’ya’yansu zuwa gabar kogi don kauce wa sake faruwar hakan.