✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya kashe mutum bakwai a Suleja

'Ya'ya hudu na wata mata sun bace bayan ruwan ya rusa gidan da suke zama a ciki.

Mutum bakwai sun mutu, wasu da dama kuma sun bace bayan an yi ruwan sama mai karfi a Karamar Hukumar Suleja ta jihar Neja.

Ruwan ya rusa gidaje sannan ambaliya ya tafi da ababen hawa da sauran dukiyoyi masu tarin yawa a ranar Asabar.

Shugaban Karamar Hukumar Suleja, Abdullahi Maje ya ce an kai gawarwaki bakwai Babban Asibitin Suleja sakamakon lamarin na yankin a Filin Polo da Rafin-Sanyi da ke wajen garin Suleja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a gida daya wata mata ‘ya’yanta hudu sun bace bayan ruwan ya rusa gidan da suke zama a ciki.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin namu cewa daga baya an tsinci gawar daya daga cikin yaran wanda dalibin jami’a ne a wani kududdufi.

Iftila’in ya faru ne a kusa da garin Madalla inda wani mutum daya ya rasu, wasu gidaje kuma suka rushe sakamakon ruwa da ambaliya a yankin Monkey Village da ke garin.