✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya lalata gida 105 a Ekiti

Akalla gidaje 105 ne suka lalace sakamakon ruwan mai hade da iska.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadin lalacewar gidaje akalla 105 a yankin Oke-Ako da ke Karamar Hukumar Ikole ta Jihar Ekiti.

Haka kuma ya lalata cibiyoyin wutar lantarki a fadin garin, lamarin da ya jefa mutanen cikin duhu.

Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, a lokacin da yake tantance asarar da aka yi a garin a ranar Lahadi, ya jajanta wa mazauna garin.

Oyebanji, wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Misis Monisade Afuye, ta bayyana faruwar lamarin a matsayin mummunar barna.

Sarkin garin Ogunbiyi Tinuade Adebayo, ya gudanar da zagayen yankunan da lamarin ya shafa.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ikole ta 2, Adeoye Aribasoye da Shugaban Karamar Hukumar Ajoni, Michael Ogungbemi su sun ziyarci yankunan don jajanta musu.

“Gwamnati ta damu da halin da aka tsinci kai a ciki, amma ina tabbatar muku da cewar za a tallafa muku.

“Za mu ba da duk wani goyon bayan da ya dace don dakile duk wani tasiri da wannan lamarin ya haifar ga rayuwarku,” in ji mataimakiyar gwamnan.

Aribasoye ya tabbatar wa jama’a cewa nan ba da dadewa ba za a kawo dauki ga wadanda abin ya shafa.

Ya bukace su da su kwantar da hankalinsu don bai wa gwamnati hadin kai domin su taimakawa wajen rage musu radadin halin da suke ciki.

Babban Daraktan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Ekiti, Mista Jide Borode, ya ce za a iya rage tasirin ruwan sama, idan mutane suka rungumi shirin dasa itatuwa na gwamnatin jihar.