✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya malale Majalisar Tarayya

Ma'aiakata sun dauki lokaci kafin su kwalfe ruwan a Majalisar.

Ruwan sama ya malale ginin Majalisar Tarayyar Najeriya a ranar Talata.

An dauki tsawon lokaci kafin ma’aikatan Majalisar dauke da robobi da injinan shara suka iya kwalfewa tare da goge ruwan.

Ga hotunan.

Ma’aikata sun fito da injina da robobi da tsintsiyoyi da sauransu domin share ruwan saman da ya malala a ginin Majalisar Tarayya.
Yadda ma’aikata suke aikin gayya da injina domin share ruwan saman da ya shiga cikin ginin Majalisar Tarayya.
Daga masu robobi zuwa masu tsintsiya, ma’aikatan Majalisar suka dukufa share ruwan da ya shiga gininta a ranar Talata.
Aiki babu kama hannun yaro wajen kwalfe ruwan saman da ya shiga cikin ginin Majalisar.
‘Yan jarida na ba wa idanunsu abinci a yayin da ake ta kokarin share ruwan.
Ruwan saman na ranar Talata ya tilasta ma’aikatan Majalisar sake shara.
An dauki tsawon lokacin kafin a gama share ruwan saman da ya shiga ginin Majalisar.