✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin dokoki 6 da CBN ya fitar kan takaita yawon tsabar kudi

Bankin kuma ya ce ’yan N200 zuwa kasa za a rika zubawa a cikin ATM

A ranar Talata Babban Bankin Najeriya (CBN), ya fitar da wasu sabbin dokoki wadanda yake so a fara aiki da su wajen hada-hada da tsabar kudi a kasar nan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin bankin ke shirin sakin sabbin takardun Naira da ya sauya wa fasali don a fara amfani da su a fadin kasar.

CBN, wanda ya sanar da hakan a cikin wata wasika ranar Talata, ya ce dokokin za su fara aiki ne daga ranar tara ga watan Janairun 2023.

Haka nan, sabbin dokokin na CBN na da nasaba kudurin da bankin ke da shi na takaita amfani da tsabar kudi wajen hada-hada.

Wadannan dokoki sun hada da:

  • Babu wanda zai cire sama da N100,000 a mako a tsakanin daidaikun mutane, sannan N500,000 ga hukumomi in dai a cikin banki ne. Mai bukatar cire sama da haka kuwa, za a dora masa harajin kaso biyar cikin 100 ga daidaikun mutane, sannan kaso 10 ga hukumomi.
  • Wanda zai ciri kudi a asusun da ba nasa ba, ba zai iya cire kudin da suka haura N50,000 ba.
  • N100,000 kawai za a iya cirewa ta na’urar ATM a mako daya, sannan N20,000 a rana daya.
  • Daga kan N200 zuwa kasa za a rika lodawa a cikin na’urorin ATM.
  • N20,000 za a iya cirewa ta POS a rana daya.
  • A duk lokacin da bukatar cire kudi fiye da abin da aka kayyade ta taso, a nan, daidaikun mutane na iya cire miliyan biyar a cikin wata daya, sannan hukumomi su cire miliyan 10, tare kuma da biyan haraji kamar yadda aka nuna a ka’ida ta (1).