✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin katinan zabe 13m muka buga —INEC

INEC na binciken zargin jami'anta da karbar na goro a aikin rabon katin zabe da ke gudana.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na bincike kan zargin jami’anta da karbar na goro a aikin rabon katin zabe da ke gudana.

Hukumar ta kara da cewa ta buga sabbin katinan zabe miliyan 13 da dubu 868 da 441 bayan kammala aikin rajistar sabbin masu zabe.

Da yake sanar da hakan, Kwamishinan INEC na Kasa kan Wayar da Masu Zabe da Yada Labarai, Festus Okoye, ya ce, “Hukumar ta damu bayan samun korafe-korafe kan nuna fifiko a wasu wuraren rabon katin.

“Duk halastattun masu rajista na da ’yancin karbar katinsu domin kada kuri’a a ranar zabe a wuraren da suka yi rajista.”

Ya ci gaba da cewa, “Don haka wajibi ne Kwamishinonin Zabe su tabbatar babu nuna wariya a rabon katin, tare da hukunta jami’ai masu kunnen  kashi.

“Domin kawar da shakku, sabbin katunan zabe miliyan 3 da dubu 868 da 441 INEC ta buga.

“Wannan adadin ya hada da sabbin wadanda suka yi rajista da wadanda suka sauya wurin zabe da kuma wadanda aka sabunta wa katinsu.”

Okoye kuma ya sanar cewa hukumar ta kara lokacin rabon katin zuwa ranar 29 ga watan Janairu da muke ciki, daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.

Hukumar ta kuma umarci jami’anta masu aikin rabon katin da su tattara duk wani korafi rashin buga kati zuwa ga shugabanninsu a jihohi domin daukar matakin da ya dace.