✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin Kwamishinoni 11 sun karbi rantsuwar kama aiki a Kano

Na zabo sabbin kwamishinonin ne bisa ga cancantar su da kuma kwarewar da suke da ita.

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci bikin rantsar da sabbin kwamishinoni  11, inda ya bayyana ma’aikatun da kowannesu zai jagoranta.

Bikin dai ya gudana ne a rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a birnin Kano.

A jawabinsa yayin taron, Ganduje ya ce ya zabo sabbin kwamishinonin ne bisa cancantar su da kuma kwarewar da suke da ita a harkokin rayuwa na yau da kullum.

Ganduje wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islama ya ce yana sa ran dukkanin kwamishinoni za su yi duk mai yiwuwa wajen ciyar da gwamnati da Jihar Kano gaba.

Ya yi fatan cewa za su yi amfani da kwarewar da suke da ita wajen kawo ci gaba a ma’aikatun da aka ratayawa nauyin kula da su.

Ganduje ya kuma bukaci da su taimaka wa gwamnatisa wajen kammala manyan aiyukan da ta faro kafin karewar wa’adinta.

Gwamnan ya gargadi da su zamo masu himmatuwa da sadaukar da kai wajen sauke nauyin da aka dora musu, inda ya taya su murna da su da iyalansu.

Sabbin kwamishinonin 11 da kuma ma’aikatun da aka rataya musu nauyin kulawarsu sun hada da; Dokta Jibril Yusuf Rurum – Ma’aikatar Noma; Ya’u Abdullahi ’Yan Shana – Ma’aikatar Ilimi; Alhaji Ibrahim Dan Azumi Gwarzo – Ma’aikatar Kasafi da Tsare-Tsare; Abdulhalim Abdullahi Liman – Ma’aikatar Raya Karkara; da Alhaji Lamin Sani Zawiyya – Ma’aikatar Kananan Hukumomin da Masarautu.

Sauran sun hada da Hon. Garba Yusuf Abubakar – Ma’aikatar Ruwa; Hon. Adamu Abdu Panda – Ma’aikatar Kudi da Ci gaban Tattalin Arziki; Hon. Sale Kausani – Ma’aikatar Gidaje da Sufuri – Alhaji Ali Musa Hamza Burum-burum – Ma’aikatar Kula da Yawun Bude Idanu da Al’adu; Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa – Ma’aikatar Lafiya da kuma Alhaji Kabiru Muhammad – Ma’aikatar Aiyuka na Musamman.