✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabbin Labarai

’Yan Majalisa Sun Ba wa Hammata Iska A Senegal

’Yan majlisa a kasar Senegal sun dambace kan zargin wani babban malamin Musulunci da ke goyon bayan jam’iyyar adawa.

’Yan majlisa a kasar Senegal sun ba wa hamata iska kan zargin wani babban malamin Musulunci da ke goyon bayan jam’iyyar adawa.

Lamarin ya faru ne yayin kuri’ar jin ra’ayi kan kasafin ma’aikatar shari’a na badi, inda wata ’yar majalisa mai suna Amy Ndiaye ta zargi wani malamin addinin Mususlinci mai suna Serigne Moustapha da ke goyon ’yan adawa da yin karya da kuma rashin mutunta shugaban kasar, Macky Sall.

Wadannan kalamai nata ne suka tunzura wani dan majalisa daga bangaren adawar, har ya gaura mata mari, kamar yadda wasu hotuna da kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna.

Bayan ya mare ta ne kuma ta wurga masa kujera sannan ta fadi kasa, kafin masu mara mata baya su taimaka mata.

Daga nan ne kuma fada ya kacame tsakanin bangarorin biyu, har sai da shugaban majalisar ya dakatar da zaman.

Tuni wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare hakkin mata suka yi tir da marin da aka tsinka wa ’yar majalisar, yayin da wasu daga cikin ’yan majalisar daga banagren adawa suka bayyana wa gidan Talabijin din kasar cewa dukkaninsu ba za su dawo aiki ba, har sai Ndiaye ta nemi afuwar malamin.

‘Ku Ilmantar Da Mata Muhimmancin zaben ’Yan Takara Nagari’

Majalisar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS) ta ce wayar da kan mata kan zaben ’yan takarar da suka cancanta a zaben 2023 na da matukar…

Majalisar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS) ta ce wayar da kan mata kan zaben ’yan takarar da suka cancanta a zaben 2023 na da matukar muhimmaci.

Shugabar kungiyar, Priscila Kuye, ta bayyana wa taron shekara da suka shirya kan muhimmacin sanya mata a sha’anin gwamnati a ranar Alhamis cewa yin hakan ya zamo dole, saboda yawan matan da ke fita yin zabe a Najeriya ya fi na maza.

“Kada ku bar wa maza komai, domin idan ana batun sha’anin mata ba su san inda ke mana kaikayi ba.

“Ku karfafa wa kanku da ’ya’yanku mata guiwar shiga harkokin siyasa, da kuma zabar mutanen da suka cancanta a 2023, domin ba kansu kadai za su zabowa ba, har da ku ma,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su kara ba wa mata gudummawar da ta dace, domin hakan ba iya rayuwarsu zai inganat ba, har ma da tattalin arziki, da zamantakewa da siyasar Najeriya.

Sojoji sun cafke ‘yan bindiga 5, sun kwato N20m a Katsina 

Sojojin sun kwato muggan makamai a hannun 'yan bindigar.

Dakarun ‘Operation Hadarin Daji’ sun kama wasu ’yan bindiga biyar a kauyen Daudawa da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina tare da kudi Naira miliyan 19.5 a hannunsu.

Daraktan Yada Labarai rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka ne a taron mako biyu kan ayyukan sojoji a fadin Najeriya a ranar Alhamis a Abuja.

Danmadami, ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri, ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022.

Ya kuma kara da cewa sojojin sun kwato wata mota da wayoyin hannu guda biyar daga hannun wadanda ake zargin.

Ya ce sojojin sun kuma kashe ‘yan bindiga uku a kauyen Yambuki da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022 yayin da wasu suka gudu da raunuka.

Danmadami, ya ce sojojin sun kwato manyan bindigogi guda 91, bindig kirar AK-47 guda 2 da kuma babura guda uku.

Ya ce sun kuma kama wani da ake zargin dan bindiga ne dauke da harsashi 269 a hanya Zariya zuwa kauyen Damari a Karamar Hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.

“Saboda haka, a tsakanin ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2022 sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda takwas, alburusai 91 da kuma bindigogi kirar gida guda biyar.

“Sojoji sun kashe ’yan bindiga 11, sun kama 10 tare da ceto wasu mutane tara a tsawon lokacin.”

Kakakin rundunar tsaron ya ce, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022 rundunar sojin sama ta kai farmaki a yankin da kasurgumin dan ta’adda, Malam Illa yake a kauyen Manawa da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Zamfara.

“Bayan harin, an tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta’adda bakwai yayin da Mallam Illa da wasu ’yan ta’adda suka tsere da munanan raunuka,” in ji shi.

Danmadami ya ce A yankin Arewa ta Tsakiya, a ranar 28 ga watan Nuwamba, dakarun ‘Operation Safe Haven’, sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne da bindigogi kirar AK-47 guda biyar da aka boye a cikin wata jaka a Gidan Ado da ke Karamar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Ya kuma ce dakarun ‘Operation Whirl Stroke’ sun kama wasu mutum biyar da ake zargin su da aikata laifuka yayin da suke sintiri a kauyukan Kwazaye, Shelena da Ukande a Karamar Hukumar Katsina-Ala a Jihar Benuwai.

Ya ce an dakarun rundunar na ci gaba da samun nasara a yakin da suke yi da masu tada zaune-tsaye a kasar nan.

Badakala: An Daure Tsohon Shugaban Jami’a Shekaru 35

Wata Babbar Kotun Tarayya ta daure tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Magaji Garba shekaru 35 kan laifin almundahanar Naira miliyan 260.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta daure tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Magaji Garba shekaru 35 kan laifin almundahanar Naira miliyan 260.

Alkalin kotun da ke Garki a Abuja, Maryam Hassan Aliyu, ce ta yanke hukuncin, bayan samun sa da aikata laifuka biyar na almundahanar da aka tuhume shi da su.

Kakakin Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Wilson Uwajaren, ya bayyana wa Aminiya cewa an kamo tsohon shugaban jami’ar ne a ranar 12 ga watan Oktoba, 2021, bisa zargin karbar wasu makudan kudade daga hannun wani dan kwangila da zummar zai ba shi kwangilar Naira biliyan uku don katange jami’ar.

Uwajeran ya ce hakan ya saba wa sashi na 1 (1) (a), da sashi na 1 (3) na Dokar Zamba da Dangoginta ta 2006.

Da fari wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai bayan gabatar da takardu da shaidu da EFCC ta yi a gaban kotun, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 35.

Hukuncin da aka yanke masa ya hada da daurin shekaru bakwai ba tare da zabin biyan tara ba a kan kowanne daga laifuka uku na farko, da kuma daurin shekaru bakwai  kan laifi na 4 da 5 tare da zabin biyan tarar Naira miliyan 10 kowanne.

Qatar 2022: Kocin Belgium, Martinez ya ajiye aiki

Belgium na da manyan ’yan wasa amma sun gaza tabuka abin arziki a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.

Kocin tawagar ’yan wasan Belgium, Roberto Martinez, ya ajiye aikinsa bayan kasar ta gaza zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya ta 2022.

Belgium na da manyan ’yan wasa irin su Hazard, De Bruyne, Lukaku, Batsuyi, Carrasco da sauransu, amma sun gaza tabuka abin arziki a gasar da ke gudana a kasar Qatar.

Belgium dai ta gaza fitowa daga rukuni bayan wasanni uku da ta kara da kasashen Kanada da Maroko da kuma Croatia, amma maki hudu ta samu, bayan cin wasa daya, rashin nasara daya da kuma kunnen doki daya.

Yanzu haka Maroko da Croatia ne suka tsallaka zuwa zagayen ’yan 16 na Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Roberto Martinez ya dade da yanke shawarar ajiye aikinsa tun kafin fara gasar a kasar Qatar.

Mahara sun kashe mutum 7, sun sace 5 a sabon hari a Sakkwato 

Maharan sun yi awon gaba da wani magidanci da matansu guda biyu.

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum bakwai tare da yin garkuwa da wasu biyar a wasu sabbin hare-hare a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Maharan sun kashe mutum shida a kauyen Bare, daya kuma a Kagara, suka sace mutum biyar, ciki har da wani magidanci da matansa biyu a kauyen Faji, sannan suka wawushe kaya da ba a san iyakarsu ba a shagunan jama’a.

Yankunan da aka kai wa harin sun hada da, Bare, Kagara, Kojiyo a Karamar Hukumar Goronyo da kuma kauyen Faji a Karamar Hukumar Sabon Birni.

Da yake tabbatar da harin, Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba wasu mutum biyar da dabbobi a kauyukan.

A cewarsa, an kai harin ne a ranar Laraba da yamma.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, amma ya ce ba shi da labari, amma ya yi alkawarin samun cikakken bayani.

PDP Ce Ta Jawo Wahalar Fetur A Najeriya —APC

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya ce gazawar jam’iyyar PDP wajen gyara matatun man Najeriya tsawon shekaru 16 da ta yi tana…

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya ce gazawar jam’iyyar PDP wajen gyara matatun man Najeriya tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki ne ya kawo karancin mai da ake fama da shi a yanzu.

A tattaunawarsa da wani gidan talabijin a Najeriya, Oshiomhole, wanda shi ne Mataimakin Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima, ya zargi PDP da lalata matatun man kasar.

“Mu tambayi kanmu, waye ya lalata matatun man tun farko? Yaya yanayinsu yake a shekarar 1999, da kuma daga wannan lokacin zuwa 2015?

“Idan PDP da ta yi mulkin shekara 16 ta gaya wa ’yan Najeriya kudin da suka barnatar wajen kula da wadannnan matatun sai ’yan Najeriya sun suma saboda yawa.

“Haka kawai (Olusegun) Obasanjo ya yanke shawarar cefanar da matatun mai, amma wanda ya gaje shi da ya zo sai ya yi mi’ara koma baya, saboda a cewarsa a watanni shida za a samu mai a wancan lokacin, wannan shi ne tushen matsalar da muka samu kanmu a ciki,” inji shi.

Don haka ya ce ya zama dole a yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa samar da sabuwar dokar man fetur da kuma jawo hankalin masu zuba jari da suka dace a bangaren, ciki har da matatar man Legas mallakin hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dangote.

Mutane Sun Gaji Da Wakokin ‘Rap’ —Wizkid

Wizkid ya ce shi kansa wakokin Rap suna gundurar sa

Fitaccen mawakin Najeriya da ke amfani da salon gambarar Afrobeat, Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya ce rashin sabunta salon wakokin ‘Rap’ ya sa mutane sun daina jin dadin su.

Mawakin ya bayyana hakan ne a ganawarsa da wata mujalla, inda ya ce shi kansa ya daina sauraron wakokin da aka yi da salon Rap, saboda gundurar sa da ya yi.

“Salon gambarar Afrobeat duniya ke yayi yanzu, domin wakar da na yi da salon sai da na sayar da kwafe miliyan biyu a Amurka kadai, kuma ko a fitattaun mawakan kasar ma ba kowanne ne ya taba sayar da makamancin haka ba.

“Wannan ya nuna inda duniya ta saka gaba a harkar waka. Ni kaina ma iya wakokin da nake ji ke nan yanzu, ba na sauraron Rap ba, saboda shekaru 10 ke nan salo daya ake amfani da shi a wakokin duk duniya.”

Mutum Miliyan 25 Ke Dauke Da Cutar AIDS A Afirka —WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce nahiyar Afirka ce ta fi yawan masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce nahiyar Afirka ce ta fi yawan masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) a duniya.

Daraktar Shiyya na Hukumar reshen Afirka, Dokta Matshidiso Moeti ce ta bayyana hakan a sakonta na ranar tunawa da masu dauke da cutar ta bana, inda ta ce mutane miliyan 25.6 ne ke dauke da cutar a nahiyar.

Dokta Matshidiso ta ce duk da yawan adadin, an samu raguwar masu cutar a yankin da kaso 44 cikin 100,  idan aka kwatanta da shekaru 10 na baya.

“A sauran larurorin ma da ke da alaka da cutar an samu saukinsu da kashi 55 a shekarun sakamakon kokarin WHO da kawayenta, wajen wayar da kan al’umma da bada tallafi da fadada sabbin dabarun kau da cutar, hadi da samar da na’u’rorin dakile ta,” in ji ta.

Sauran abubuwan da suka taimaka a cewarta sun hada da samun karin magunguna masu arha, wuraren gwaji da kayan aiki da ma tallafi da yankin Arewa maso Yamma da Afirka ta Tsakiya ke samu.

Ana gudanar da bikin ne a duk ranar 1 ga watan Disamba domin jawo hankalin duniya game da cutar, da tunatar da masu ruwa da tsaki cewa har yanzu tana nan a duniya.

An yi wa ’yar jaridar Najeriya, Toke Makinwa fashi a London

Makinwa ta bayyana kaduwarta da fashin da aka yi mata a birnin London na kasar Birtaniya

Fitacciyar ’yar jaridar nan, Toke Makinwa, ta ce ’yan fashi sun raba ta da wasu muhimman kayayyakinta a birnin London.

Makinwa, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo da talabijin da ta sanar da fashin da aka yi mata ne ta shafinta na ‘Snapchat’.

Ta ce, “Yanzu aka yi mini fashi a London, na ma rasa abin cewa. Ta yaya hakan za ta faru da ni?” inji ta.

Wasu ra’ayoin da aka bayyana a karkashin sakon da Toke Makinwa ta wallafa sun nuna London  da Legas tamkar wa da kani ne inda ake fama da bata-gari, kuma akwai ’yan Najeriya mazauna birnin da daman gaske.

Idan za a iya tunawa, kwanan nan gwamnatin Najeriya ta shawarci ’yan aksar masu shirin zuwa Amurka da Birtaniya da wasu kasashen Turai da su yi hattara da barayi a can.