✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin masu yi wa kasa hidima 21 sun kamu da COVID-19 a Taraba

Yanzu haka an killace wadanda suka kamu a sansanin basu horo.

Kimanin sabbin matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) 21 da aka tura Jihar Taraba a rukunin ‘B’ zango na biyu ne suka kamu da cutar COVID-19.

Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya a Jalingo cewa an tabbatar da kamuwar matasan ne bayan tilasta wa dukkan matasan da masu ziyara yin gwajin cutar ga kafin shiga sansanin da ake basu horon.

Majiyar ta kuma ce wadanda suka kamun suna can an killace su a cibiyar killace masu cutar a cikin sansanin da ke garin Sibre a kan hanyar Jalingo zuwa Wukari.

“Dukkan mutum 21 na cikin sabbin matasan da ba a ma kai ga yi musu rijista a sansanin ba,” inji majiyar.

Sai dai ya ce za a kyale su su ci gaba da harkokinsu su a cikin sansanin da zarar an sake gwada su kuma sakamakon gwajin ya nuna ba sa duke da cutar nan gaba.