Daily Trust Aminiya - Sabon albashi: Tsoffin sojoji su yi zanga-zanga
Subscribe

Wasu daga cikin tsofaffin sojojin a lokacin zanga-zangar

Sabon albashi: Tsoffin sojoji su yi zanga-zanga

Tsoffin Sojojin Kasa na Najeriya sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan su hakkokinsu da sabon mafi karancin albashin da Shugaba Buhari ya ba da umarni tun a shekarar 2019.

Dattijjan, cikinsu har da wadanda suka halarci yakoki sun sun yi dafifi ne a hedikwatar Ma’aikatar Kudi ta Tarayya suna daga kwalaye masu dauke da rubutun nuna damuwarsa da neman a biya su hakkokinsu.

“A biya mu sabon mafi karancin albashi da aka amince da shi tun watan Mayun 2020, tsoffin sojoji na mutuwa” da kuma “Shugaba Buhari ya jikan mu ya biya sojojin da suka yi ritaya alawus dinsu na (SDA),” kadan ne daga cikin rubuce-rubucen da ke jikin kwalayen.

Da yake jawabi da yawun zanga-zangar, Shugaban Kungiyar kula da Jin Dalin Tsoffin Sojoji da Iyalensu, MWO Anthony Agbas, ya ce zanga-zangar kira ce ga gwamnati da ta rika kulawa da su ba watsi da su ba.

MMO Agbas ya koka cewa har yanzu ba a biyan wasu daga cikinsu da suka yi yakin basasar Najeriya fansho ba.

Ya roki Gwamnati da ta biya sa alawus din su na SDA, wanda aka tsara domin hana su amfani da kwarewarsu ta aikin soja wurin zama barazanar tsaro ga kasa bayan sun yi ritaya.

Shugaban Kungiyar ya ce tun daga watan Nuwamban 2017 zuwa yanzu, ’yan tsiraru daga cikin tsoffin sojoji ne Ma’aikatar Tsaro take biyan su kudinsu na SDA.

“Muna rokon a biya mu bashin cikon sabon kudin fanshonmu na wata 20 da aka amince da shi tun watan Afrilun 2019 ga tsoffin hafsoshi da sojoji da ke raye,” inji shi.

Wasu daga cikin tsoffin sojojin

Ya kuma koka kan zaftarar da ake wa fanshon tsoffin sojojin da suka yi ritaya saboda larurar rashin lafiya.

“Muna neman a dawo da tsoffin sojojin da aka yi wa ritaya saboda rashin lafiya kudaden da ake yankewa daga fanshonsu na tsawon shekara 40.

“Sun karar da kuruciyarsu wajen yi wa Najeriya yakin basasa domin tabbatar da zamanta a matsayin dunkulalliyar kasa; amma abin takaici wasunsu N10,000 ake biyan su, bisa hujjar cewa an yi ta biyan su fiye da abin da ya kamata sama da shekara 40.

“Muna rokon Shugaban Kasa ya ba da izinin a fara biyan fansho ga tsoffin sojoji da hafsoshin da suka yi ritaya bayan sun yi yakin basasa amma ba a biyan su fansho.

“Kai da kanka ka ba wa Hukumar Fansho Sojoji (MPB) umarnin ta tantance su a watan Oktoban 2015.

“Mutanen nan suna rayuwa a cikin wahala kuma ka san irin wahalar da suka sha a lokacin yakin basasa.

“Amma a matsayinmu na wadanda muka yi yakin basasa domin tabbatar da kasar nan  hade, ba za mu yi duk wani abun da zai zama barazana ga tsaron kasarmu ba,” inji shi.

Tsoffin sojojin dauke da kwalaye a lokacin zanga-zangar lumanar a Hedikwatar Ma’aiktar Tsaro da ke Abuja.
More Stories