✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon harin bom ya jikkata mutum 9 a Taraba

Kwana uku bayan makamancinsa da kungiyar ISWAP ta kashe mutum 30 a wata mashaya

Wani harin bom da aka kai da dare ya yi sanadiyyar jikkata akalla mutum tara Jihar Taraba.

Bom din ya tashi ne ranar Juma’a da dare a unguwar Nukkai da ke kan iyakar Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar wa wakilinmu cewa mutum tara sun samu rauni a harin bom din.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu cikakken bayani, amma Aminiya ta gano an kai harin ne a kusa da wani gidan giya, kuma ya farfasa jikin gini.

Harim na zuwa ne kwana uku bayan wani makamancinsa da kungiyar ISWAP ta kai wata mashaya a jihar ya kashe mutum 30.

Daga baya kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa kafirai ne hadafinta a harin da mayakanta suka kai mashayar.