✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon rikici ya kunno kai a PDP ta Kano kan ba ’yan takara tuta

Shugaban jam'iyyar ya ce sam ba da tutar haramtacce ne

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya nesanta kansa da sauran shugabannin jam’iyyar na jiha daga gabatar da tutoci ga yan takarar jam’iyyar a jihar.

A ranar Asabar din da ta gabate ce dai tsagin tsohon Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Aminu Wali, ya raba tutoci ga Mohammed Sadiq Wali a matsayin dan takarar Gwamnan Kano da sauran ’yan takara.

A martanin da shugaban ya sanya wa hannu da kansa a Kano, Sagagi ya bayyana taron a matsayin wani yunkuri na yaudarar ’yan jam’iyyar gabanin zaben 2023.

Shehu Sagagi ya kara da cewa duk wasu al’amura da suka shafi ’yan takarar jam’iyyar PDP a Kano za su ci gaba ne bayan hukuncin kotu da ake sa rai yau [Litinin] 19 ga watan Disamba 2022.

“A halin yanzu, ba za mu iya ba wa kowa daga cikin ’yan takarar Gwamnan Kano su biyu tuta ba, domin suna gaban kotu suna jiran hukunci, a matsayinmu na ’yan kasa masu bin doka da oda, dole ne mu jira sakamakon hukuncin kotun da ke tafe nan gaba kadan kafin mu yi wani abu da ya shafi ’yan takara,” inji Sagagi.

Shugaban ya kuma tabbatar wa da ’yan jam’iyyar ta PDP na Kano cewa bayar da tutoci da aka yi a ranar Asabar an yi shi ne ba tare da amincewar shugabannin jam’iyyar na jiha ba.

Daga nan sai ya bukaci jama’a da su yi watsi da taron domin ba komai ba ne illa nuna rashin mutuntawa ga doka da oda ta yadda zai haifar da rarrabuwar kawuna da rage damar cin zabe ga jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

“Ina so in tabbatar wa kowa da kowa cewa za mu sanar da rana da lokacin da za a mika tutar jam’iyyar a hukumance ga duk ’yan takarar PDP bayan hukuncin kotu insha Allahu,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP da magoya bayan jam’iyyar a jihar Kano da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda tare da yin watsi da duk wasu bayanan da ba su fito daga jam’iyyar ba.