✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon salon bangar siyasa a Soshiyal Midiya

Ya kamata matasa masu bangar siyasa ta intanet su san cewa soshiyal midiya ba jam'iyyar siyasa ba ce, ba katin zabe ba ce ko rumfar…

Wani sabon salon yakin neman zabe da ’yan siyasa a Najeriya suka bullo da shi shi ne na amfani da wasu gungun matasa wajen taimaka musu yada manufofinsu da taya su neman goyon bayan jama’a ta hanyar amfani da zaurukan sada zumunta a kafafen sadarwa na zamani.

Raja’ar da mutane suka yi wajen mu’amala da wadannan zaurukan sada zumunta irin su Facebook da Twitter da Instagram da WhatsApp da sauran su, da dama ya sa harkokin sadarwa da isar da sakonni ba na abokai da kungiyoyin matasa kadai ba, hatta kafafen sadarwa da ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun bi sahu, wajen bude shafuka da zauruka daban-daban, don isa ga jama’a da kuma tattaunawa da muhawara kan ayyukansu.

’Yan siyasa na amfani da wadannan matasa ne saboda jan hankalin sauran jama’a su fahimci tsare-tsarensu da manufofinsu na siyasa, musamman kasancewar matasan su ne suka fi mu’amala da wadannan shafuka, saboda abubuwan da tsare-tsaren da manhajojin ke ba su na nishadi da musayar sakonni na abokantaka da soyayya da debe kewa.

Sakamakon yadda akasarin wadannan matasa ke zaune babu ayyukan yi, ko babu wasu nauye-nauye a kansu da za su dauke musu hankali, ko kuma dai dalibai ne da harkar karatu ta tsaya, saboda yajin aikin malamai ko kuma rashin wadatar iyaye.

Wannan yana kara nuna irin yadda ’yan siyasa ke bin kowacce hanya don ganin sun cimma burinsu.

A baya an ga yadda ’yan siyasa suka rika amfani da matasa wajen ba su kayan shaye-shaye suna yi wa kansu illa da sunan bangar siyasa, ana tura su tarwatsa cibiyoyin zabe da satar akwatin zabe da kisa ko yi wa abokan adawa lahani.

Mun ga yadda ’yan Jagaliyar siyasa a Kano, ’yan Kalare a Gombe, ’yan Gunda a Bauchi da ’yan ECOMOG a Borno suka haifar da babban kalubalen tsaro a jihohinsu, wanda har yanzu ba a kammala warwarewa ba.

Za a iya cewa, wannan salo na amfani da soshiyal midiya ya kawo sauyi a harkar jagaliyar siyasa, inda yanzu harkar ta koma bayan fage ake yin ta a wayoyin hannu ba tare da makami ko shaye-shaye ba.

Sai dai kuma wasu na cewa, alkalami ya fi takobi kaifi — Amfani da kalaman batanci da cin zarafin juna da yada labaran karya don lalata kima da mutuncin wani dan siyasa ko abokin adawa, ita ma illa ce babba, da ke da hadari ga ci gaban al’umma da zaman tare.

Babu wani dan siyasa yanzu da za ka ga ba shi da wasu rukunin matasa da ya ware yana ba su wasu ’yan kudade suna sayen data don taimaka masa wajen yada manufofinsa, inda kuma za ka ga wani lokaci har da tayar da muhawara mai zafi tsakanin magoya bayan wannan dan takara zuwa wancan.

Kowane bangare na fifita dan takarar da suke goyon baya, ko dai saboda wasu ayyuka da ya yi wa jama’a a baya na ci gaba, ko yawan mukaman da ya rike a baya da gogewarsa, ko yadda yake nuna kishin sa ga jama’ar yankin sa, addininsa ko tallafawa matasa da ayyukan yi.

Wadannan na daga cikin abubuwan da akasari aka fi amfani da su wajen yakin neman zabe a zaurukan sada zumunta.

Kuma hakan a ra’ayin wasu matasan ’yan siyasa yana tasiri sosai, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu, musamman idan aka yi dace da gwanayen iya rubutu da mayar da martani ga duk wani motsi na abokan adawa, wanda kuma yake da mabiya ko abokai da dama, ta yadda da zarar ya tura sako daya cikin ’yan mintina kalilan zai jawo muhawara da tattaunawa a kai.

Usman Bigi yana daga cikin matasan da suke wannan aiki na siyasar soshiyal midiya, ya kuma bayyana min cewa babu shakka ana samun alheri kadaran-kadahan, amma yawanci matasa sha’awa ce take kai su ga shiga wannan harka saboda suna son su ma a rika damawa da su, musamman idan kakar zabe ta zo, don kada a yi babu su.

Shi kuwa Bala Sawaba matashin dan siyasa ne da koyaushe za ka same shi a gidan wannan dan siyasa zuwa wancan, yana abin da ake cewa kala, shi da wasu abokansa, don samun na sayen data, da shiga cikin manyan ’yan siyasa ana tattauna hanyoyin cin nasarar zabe da nakasa tasirin abokan adawa.

A ganinsa duk wani matashi da yake da burin yin siyasa to, dole ne ya zama yaron wani, don ya koyi dabarun siyasa, ya samu gogewa kuma a san shi sosai a harkar.

Ummu Ayman matashiya ce da ake gogawa da ita a wannan fage a cikin mata kalilan da suke ba da gudunmawa wajen muhawara kan ’yan siyasa a zaurukan sada zumunta, ta yi fatan ’yan siyasa ba za su manta da su ba bayan samun nasarar zabe, domin yabawa da irin rawar da suka taka; A maimakon ko da yaushe a bar su da tura mota tana tashi ta bade su da hayaki, ba za a sake waiwayar su ba sai wani zaben ya zo.

A dalilin haka ne, wani matashin dan siyasa a Jos, Malam Abdulhadi Abdullahi, ya fito da wani salon jan hankalin matasa inda yake kiran matasa masu siyasar soshiyal midiya su tabbatar sun mallaki katin zabensu a hannu, domin ranar zabe su yi amfani da shi wajen kawo sauyin da suke da burin gani a siyasar yankinsu.

Kuma da alamun wannan salo nasa yana samun karbuwa, a wajen wasu matasan.

Masu hikimar magana dai na cewa, zamani riga ne. Allah kuma Shi ne zamani. Babu wanda zai yi fada da abin da zamani ya kawo, amma kuma ba zai yiwu a yi shiru a kawar da kai ba.

Akwai bukatar matasa su samu jagoranci da saiti kan yadda za su tafiyar da wannan harka ta soshiyal midiya da kauce wa hadarin ta; Don ya kasance ba a fagen siyasa kadai ba, har a sauran harkokin su na rayuwa zai zama musu mai amfani.

Amma a lokaci guda kuma ya zama wajibi a tunatar da matasa cewa, Facebook ko Twitter da WhatsApp ba Jam’iyyar siyasa ba ce, kuma ba katin zabe ko rumfar zabe ba ne.

Dole in suna bukatar yin siyasa sosai, su je su yi rajista da wata jam’iyyar siyasa da suka aminta da tsarinta da manufofinta.

Kuma su tabbatar suna da katin zabe a hannunsu, don ya zama makaminsu na kawo sauyi a al’amarin rayuwarsu da al’ummarsu.

Sannan su tabbatar sun koma makaranta ko kuma sun kammala karatunsu, ta yadda ko da taimaka musu wani dan siyasa zai yi, zai yi musu taimakon da zai inganta rayuwarsu ne, wajen sama musu aikin da ya dace da wahalar da suka yi masa ta yakin neman zabe.

Masu sana’o’in dogaro da kai kuma su dage wajen rike sana’o’insu da mutunci, kada su bari siyasa ta dauke musu hankali daga abin da yake tsare mutuncinsu, da tallafawa iyalansu.

Domin duk wani abu da za su samu daga wani dan siyasa, ba wani abu ne da ya kai ya kawo ba.

Har wa yau, ina mai ba da shawara, a yayin da ake tattaunawa game da gudunmawar ’yan siyasa a rika kawo batutuwa masu muhimmanci da za a rika kalubalantar ’yan siyasa a kai, abubuwan da za su kawo wa al’umma cigaba da makoma ta gari.

A maimakon a yi ta zuga su ana yaba wa ayyukan da suka yi na neman suna ko son a sani, ba na tsakani da Allah ba, a mafi akasarin lokuta!

A kauce wa rubuce-rubucen hassala juna ko tsokano fitina don a ci zarafin wani ko aibata shi — Abin da ka iya haifar masa da mummunan suna da lalata mutuncin sa ba kawai a siyasance ba, har ma da martabarsa a idon al’umma da ta iyalansa.