✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Shugaban Kenya ya soke biyan tallafin man fetur a kasar

Ya ce kasar ba za ta ci gaba da biyan tallafin ba

Kwanaki kada bayan rantsar da shi, sabon Shugaban Kasar Kenya, William Ruto ya ce ba zai yiwu ya ci gaba da biyan kudin tallafin man fetur ba.

Wasu daga cikin manyan kalubalen da sabon Shugaban zai fuskanta sun hada da sauko da farashin man fetur da abinci a kasar da ta fai kowacce girman tattalin arziki a Gabashin Afirka.

Kazalika, zai yi fama da biyan tallafin mai, wanda masana suka yi hasashen zai iya yi wa lalitar kasar karkaf, ga kuma bashin da Shugaban ya gada, Uhuru Kenyatta, ya bar masa.

Da yake jawabi bayan an rantsar da shi ranar 13 Talata, William Ruto, ya ce kudaden tallafin ana karkatar da su sannan kuma suna haddasa zirarewar man ta bayan fage.

To sai dai a ranar Laraba, Hukumar Kula da Makamashi da Man Fetur ta kasar ta kara farashin man fetur da dizal da kananzir, wadanda galibi da su ake girki a kasar.

Farashin man fetur dai ya tashi da kaso 13 cikin 100, na dizal da kaso 18 cikin 100, sai na kananzir da kaso 16, in aka kwatanta da watan da ya gabata.

Hukumar dai ta cire tallafin a kan man fetur, kodayake ta ce za a ci gaba da biya a kan man dizal da kananzir.

Masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar janye tallafin ya sa farashin kayayyaki su dada yin tashin gwauron zabo daga kaso 8.5 cikin 100 da aka samu a watan Agusta.

A watan Yunin da ya gabata, Ma’aikatar Kudin Kasar ta ce ba ta da isassun kudaden da za ta ci gaba da biyan kudin tallafin man fetur din, musamman idan farashinsa ya ci gaba da tashi.