✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon ‘virus’ din wayoyi ya bulla a Najeriya —NCC

Ana daukar virus din mai suna AbstractEmu daga Play Store kuma yana birkita saitin waya.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ja hankalin ’yan Najeriya kan wani sabon virus da ya bayyana wanda ke da hatsari ga wayoyin zamani, wato ‘Smart Phones’.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun Hukumar NCC, Ikechukwu Adinde, ya fitar a ranar Talata.

Ya ce Kwamitin Agajin Gaggawa ta Kwamfuta ta Najeriya (ngCERT), wadda Gwamnatin Tarayya ta kafa don kula da hadarin barazanar yanar gizo a Najeriya, ce ta gano hakan.

“Virus din wanda aka masa suna da  AbstractEmu zai iya shiga tare da birkita saitin waya ba tare da mai wayar ya sani ba,” cewar kakakin hukumar.

Ya kara da cewa an gano cewa akan dauki virus din ne ba tare da an sani ba a Google Play Store da wasu kafofin sauke abubuwa a kan waya kamar Amazon Appstore da Samsung Galaxy Store, da sauran kafofi da dama ba a san su sosai ba kamar Aptoide da APKPure.

Hukumar ta ce domin kare wayoyi daga kamuwa virus din na AbstractEmu, mutane su yi taka tsantsan wajen sanya manhajojin da ba su san su ba ko kuma wadanda ba su saba ganin su ba, sannan su kula sosai da yanayin wayoyinsu a yayin da suke amfani da su.

A karshe NCC ta ce duk wanda yake tunanin wayarsa ta kamu da virus din to ya hanzarta yi wa wayarsa ‘restore’ kafin abin yayin kamari.