✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar matatar mai za ta fara aiki a Satumba

Hukumar kamfanin sabuwar matatar mai da ake ginawa a jihar Edo ta ce aikin ya kai kashi 90 cikin 100 kuma zai fara aiki nan…

Hukumar kamfanin sabuwar matatar mai da ake ginawa a jihar Edo ta ce aikin ya kai kashi 90 cikin 100 kuma zai fara aiki nan da karshen watan Satumba.

Shugaban sashen kula da nagartar ayyuka da hulda da jama’a na kamfanin, Mista Segun Okeni, shi ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci ‘yan majalisar jihar zuwa wani rangadin matatar da ke garin Ologbo, Karamar Kukumar Ikpoba-okha, a ranar Talata.

Ya ce matatar na da karfin tace ganga 60,000 a kullum nan ba da jimawa ba.

Sai dai ya ce kashin farko na aiki na hankoron ganga 1,000 a kowace rana, sai 6,000 a kashi na biyu har a kai ga fara tace ganga 60,000 din daga bisani.

Ologbo ya kuma yi bayanin cewa kamfanin zai rika tace man dizel, fetur da kuma gas da zarar ta fara aiki.

Ana sa ran matatar za ta rika samu man da za ta rika tacewa daga kamfanin mai na NPDC wanda ke kusa da ita.

“A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, masu zuba jari kimanin 55 ne aka ba lasisin kafa sabbin matatun mai a Najeriya, amma zuwa yanzu guda biyar ne kacal suka fara aikin ginawa ko suka kammala.

“Amma duk a cikinsu aikin matatarmu ya fi sauri. An ba mu lasisi a shekara ta 2018 kuma a watan Oktoban 2019 muka fara gini, a kasa da shekara daya da farawa kuma ga shi mun shirya fara aiki.

“Tuni muka dauki mutane sama da 300, yawancinsu kuma daga yankunan da ke da makwabtaka da mu a cikin jihar ta Edo”, inji Mista Segun.