✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar Shekara: Mun cafke jiragen Rasha 12 —Ukraine

Duk da haka sojojin na Ukraine sun taya dakarunsu murnar shiga sabuwar shekara.

Jiragen yaki 45 marasa matuka mallakin Rasha sun kai wa Ukraine hari a daren sabuwar shekara, amma hukumomin Ukraine sun ce tuni dakarunsu suka yi nasarar cafke jirage 12 daga cikinsu.

Rundunar sojin kasar Ukraine ta yi zargin cewa hare-haren na da hadin bakin kasar Iran da ke goya wa Rasha baya a wannan rikici.

Hukumomin Ukraine sun ce Iran ta saba samar wa Rasha da jiragen yakin da take yi wa kasar kutse da su.

Sai dai duk da haka sojojin na Ukraine sun taya dakarunsu murnar shiga sabuwar shekara tare da karfafa musu gwiwar nasara.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da a gefe guda, Ukraine ta zargi Rasha da kai mata hare-hare da makamai masu linzami guda 20 a ranar Lahadi da ke zama ranar farko ta sabuwar shekara.

Haka kuma, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasarsa ba za ta taba yafe wa Rasha ba kan wadannan hare-hare da ta kai a cikin birnin Kiev da kuma yankin Zaporizhzhya da ya kunshi cibiyar nukiliya.

Rasha ta kai wasu munanan hare-hare a Ukraine a yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kalilan a shiga sabuwar shekara ta 2023.

Shugaban Ukraine ya wallafa haka a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa bai dace hukumomin Moscow su kai wa Ukraine hari da makamai masu linzami ba a daidai lokacin da jama’a ke tsaka da shirin shiga sabuwar shekara.

Ya ce babu wani mutum a doron kasa da zai iya kawar da kai daga wannan abin da ya kira “danyen aikin” da Fadar Kremlin ta aikata.