✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar Shekarar Musulunci: Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu a Kano

Gwamnati ta bayar da hutun ne albarkacin sabuwar shekarar

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin, daya ga watan Agustan 2022 a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar da maraicen Laraba a Kano.

Ya ce Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya daukacin al’ummar Musulmin jihar murna zagayowar shekarar mai cike da albarka.

Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da lokacin wajen neman yafiyar Ubangiji musamman kan kalubalen tsaron da kasar nan ke fama da shi.

Sanarwar ta kuma ce Gwamnan ya yi kira ga duk wadanda ba su mallaki katin zabensu ba da su gaggauta yin hakan don samu su kada kuri’arsu a zaben 2023 da ke tafe.

Sabuwar shekarar Musuluncin ta bana dai, wacce za ta fara a farkon watan Almuharram, za ta shiga ne ranar Asabar, 30 ga watan Yulin 2022