✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sace Dalibai: Gwamnati Ta Bude Makarantu 45 Da Ke rufe A Zamfara

Yanzu dai jimillar makarantu 30 ne kadai ke rufe

Ma’aikatar Ilimi ta Zamafara, ta ce gwamnatin jihar  ta ba da umarnin bude makarantu 45 da a baya tabarbarewar tsaro ya sa aka rufe su.

Sakataren ma’aikatar, Kabiru Attahiru ne ya bayyana hakan a Gusau, yayin da yake karbar jami’an sashen Fasaha na Ilimi a jihar (EiE), yayin ziyarar ban girma da suka kai ma’aikatar.

Gwamnatin jihar ta rufe makarantun ne a watan Satumbar 2021, bayan sace daliban Makarantar Gwamnati ta Kaya da ke Karamar Hukumar Maradun da ’yan bindiga suka yi.

“Mun raba bude makarantun zuwa kashi uku, inda muka ba su suna da launi, wato kore, da kawaya, da kuma ja.

“Masu alamar kore su ne muka bude yanzu, kuma suke a wuaren da ba a fuskantar barazanar tsaro.

“Sai masu launin rawaya da ke fuskanta ’yar karamar barazana, sannan sai jajaye da suke fuskantar babban kalubalen tsaron.

“Yanzu dai jimillar makarantu 30 ne kadai ke rufe, amma muna fatan a kara samun ingantar harkokin tsaro domin su ma mu bude su baki daya”,  inji shi.