✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sadio Mane ya dawo atisaye a Bayern Munich

Mane ya ji ciwon da ya hana shi wakiltar Senegal a Gasar Kofin Duniya.

Sadio Mane ya dawo atisaye a Bayern Munich, bayan raunin da ya yi jinya ta tsawon watanni.

Daf da za a fara Gasar Kofin Duniya a cikin Nuwambar 2022 a Qatar, Mane ya ji ciwon da ya hana shi wakiltar Senegal a babbar gasar tamaula ta duniya.

A wani faifan bidiyo da Bayern ta saka a shafinta na Twitter, an ga tsohon dan wasan Liverpool na atisaye a cikin filin Munich da kankara ta lullube.

Mane, mai shekara 30 ya ji rauni a kafarsa ta hagu a wasan da Bayern ta lallasa Werder Bremen 6-1 ranar 8 ga watan Nuwambar 2022.

Daga nan ne aka yi masa tiyata, wanda ya yi jinyar da ta hana shi buga Gasar Kofin duniyya da aka yi a Qatar, wanda Argentina ta lashe na uku jumulla.

Kociyan Bayern, Julian Nagelsman ya fada a cikin Janairu cewa yana sa ran Mane zai buga wa Bayern haduwar da za ta yi da Paris St German ranar 8 ga watan Maris a Gasar Zakarun Turai.

Sai dai kuma Mane bai buga wa Bayern wasan da ta karbi bakuncin Cologne ba ranar Talata, domin bai kammala komawa kan ganiya ba.