✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sadiya Adamu Aliyu: Gata ga wadanda aka yi wa fyade

Sadiya Adamu Aliyu lauya ce kuma mai fafutukar kwato hakkin marasa galihu

Daya daga cikin matsalolin da suka sha wa al’umma kai a wannan zamani ita ce karuwar fyade, musamman wa kananan yara – saboda haka samuwar mutane irin su Sadiya Adamu Aliyu ta dauke wa al’umma wani babban nauyi.

Kungiyar Barista Sadiya mai suna Initiative for the Support of Victims of Sexual Abuse, Orphans & Less Privilleged (ISSOL) tana kula da bukatun wadanda aka yi wa fyade da marayu da marasa galihu.

Dubban yaran da wannan ibtila’i ya shafa ne kungiyar ta tallafa wa zuwa yanzu.

Bayan haka, Tauraruwar mamba ce a gamayyar kungiyoyi masu yaki da fyade da cin zarafin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wato Coalition Against Rape and Violence (CARAV), kuma wakiliya a hukumar daraktocin cibiyar bunkasa sadarwa ta Vision Center for Communication and Development Advocacy (VICCDA).

Aure ba ya hana karatu

Tana kuma cikin kwararrun da suka kafa Zauren Kano 9 (wato Kano 9 Forum ko K9 Forum) don gano da kuma karbo yaran nan da aka sace a Kano aka kai su wasu jihohi a Kudu.

Barista Sadiya Adamu Aliyu lauya ce, kuma kyakkyawar abar misali, ta bayyana cewa aure ba ya hana ’ya’ya mata karatu (kamar yadda karatu ba ya hana aure), don kuwa shekararta 10 ke nan a gidan miji.

Ma’ana daukacin karatunta na lauya tana gidan miji ta yi sannan duk fafutukar da take yi a yanzu tana da ’ya’ya hudu a gabanta.

Da za ku ci karo da Barista Sadiya, idan kuka gan ta da abaya kada ku yi mamaki, domin kayan da ta fi sha’awa ke nan, kamar yadda a abinci ta fi kaunar burodi da shayi.