✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai an kula da hakkin marayu Najeriya za ta zauna lafiya — Sheikh Bala Lau

Ya ce dukkan kokarin gwamnati ya gaza kaiwa ga cin ma ruwa a bangaren

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta ce samun zaman lafiya a kasar nan zai yi wuya, matukar al’umma da gwamnatoci suna watsi da hakkokin marayu da sauran mabukata.

Shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin taron ba da tallafin kayan Sallah ga marayu sama da 1,000 da kungiyar ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata, a harabar hedikwatarta ta kasa da ke Abuja.

Sheikh Bala Lau ya ce marayu da sauran raunana suna bukatar tallafin jama’ar da suke zaune a cikinsu don tabbatar da cewa sun samu ilimi da sana’a don amfanar kansu da ita kanta al’ummar,
maimakon barinsu kara-zube.

“Hakan na iya kai su ga fadawa hannun kungiyoyin ta’addanci ko na ’yan daba a dalilin jahilci ko rashin abin hannu,” inji malamin.

Ya ce baya ga tallafin da kungiyar ta bai marayu a yayin taron da ya hada da ba kowane a cikinsu buhun shinkafa mai
nauyin kilo 25 da yadi biyar na shadda ga maza ko turmin atamfa ga mata, sai kuma Naira dubu biyar na dinki, Sheikh Bala Lau ya ce kungiyar za ta fara daukar nauyin karatun marayu kamar
100 a yankin Abuja kadai, da hidimar auren ’yan mata 20 daga kowace jiha, sai kuma ba da horon sana’a ga iyayensu mata tare da ba su jari don kula da hidimarsu.

Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Birnin Tarayya, Abuja, Alhaji Abdullahi A. Diggi ya ce daga fara azumi zuwa Juma’ar da ta gabata, kwamitin ya samu tallafin Naira miliyan 30 inda aka yi sayayyar kayan da aka raba tare da kudi da suka kai na Naira miliyan 22 da doriya.

Ya ce wadanda aka tallafawa, sun fito ne daga yankunan kananan hukumomin Abuja 6, kuma ragowar kudin da wanda
ake tsammani samu kafin rufe tafsirin bana, za a yi amfani da su ne wajen sauran ayyukan da suka hada da tallafa wa iyayen marayun kan sana’a da karatun yaransu sai kuma aure ga ’yan
mata marayu.

Sheikh Kabir Haruna Gombe, wanda ya jagoranci yekuwar tara kudin a yayin tafsiri da ya yi na bana a Abuja, ya ja hankalin al’umma kan muhimmancin kula da marayu da sauran raunana.

Ya ce Gwamnatin Najeriya ta biya kusan dukkan bukatun kudi kan yaki da matsalar tsaro, ba tare da cikakken nasara a kai ba.

“To yanzu lokaci ya yi da ya kamata a hada da tallafa wa bukatun marayu da sauran mabukata don neman tausayawar Allah a kai na kawo karshen matsalar,” inji malamin.