✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai an tashi tsaye wajen dakile shan miyagun kwayoyi —Saraki

A matsayina na likita, na san yadda shan miyagun kwayoyi ke tarwatsa al'umma.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Abubakar Bukola Saraki ya nemi a tashi tsaye don kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Saraki ya yi wannan kira ne a taron shekara na masu gidajen talabijin da rediyo na Arewacin Najeriya da aka gudanar ranar Litinin a dakin taro na Otal din Bristol da ke Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito Saraki ya yi jawabi ne mai taken ‘SHAN MIYAGUN KWAYOYI A AREWA, DA RAWAR DA KAFAFEN WATSA LABARAI ZA SU TAKA WURIN DAKILE ANNOBAR’ a wurin taron Kungiyar ta NBMOA.

Bukola Saraki wanda ya samu wakilcin Tsohon Shugaban Majalisar Jihar Kwara, Hon. Ali Ahmed ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai da su tashi tsaye wurin kawo karshen annobar shan miyagun kwayoyi.

Ya ce: “Na yi matukar murnar kasancewa a wurin wannan taro na masu juya kafafen watsa labarai a Arewacin Najeriya, inda za mu tattauna muhimmin lamarin da ke ci wa kowa tuwo a kwarya.

“Maudu’in wannan taro na yau, yana matukar tada min hankali duk lokacin da na tuna da irin illar da yake yi wa al’umma. A matsayina na likita, na san yadda shan miyagun kwayoyi ke tarwatsa al’umma.

“Ina son tabbatar mana da cewa, shan miyagun kwayoyi na kara ta’azzara annobar garkuwa, ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a Arewa,” inji shi

Saraki ya kawo alkalumma na yawan wadanda ke shan miyagun kwayoyi a Arewa, inda ya ce a shekarar 2021 an tantance kaso 14.4 na ‘yan Najeriya ke shan miyagun kwayoyi, ‘yan shekara 15 zuwa 64.

Haka nan kuma, tsohon gwamnan na Jihar Kwara ya kawo adadin gidajen gyaran hali da ake da su a fadin Arewa.

Daga karshe ya bayar da misalai na hanyoyin da za a bi wurin saita halin wadanda suka jefa kansu a wannan mummunar hanya ta shaye-shaye.

 Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya kasance babban bako kuma mai masaukin baki a wurin taron.