Sai Buhari ya bar mulki za a ga amfaninsa — Bashir Ahmad | Aminiya

Sai Buhari ya bar mulki za a ga amfaninsa — Bashir Ahmad

    Abubakar Muhammad Usman

Mai Ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya ce ’yan Najeriya ba za su ga alfanun mulkinsa a yanzu ba sai bayan ya kammala wa’adinsa a 2023.

Ahmad ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, inda ya ce Buhari ya dora Najeriya akan turbar da ta dace.

Ya ce, “Turbar da Shugaba Buhari ya dauka ba za a ga amfaninta a fili a yanzu ba sai bayan ya bar mulki.

“Ya dora kasar nan akan kyakkyawan tsarin da duk shugaban da ya zo zai dora. Wasu tsare-tsaren na gyara ba sa yiwuwa sai an sha wuya, amma kuma daga karshe za a ci moriyarsu na dindindin,” kamar yadda ya wallafa.

Hadimin na wannan jawabi ne bayan suka da shugaba Buhari ya sha, game da hirarsa da ya yi a gidan talabijin na Channels, inda wasu ke ganin ya nuna rashin kwarewa da sanin makamar aiki ta shugabanci.

A yayin hirar, Buhari ya tattauna batutuwa da dama wanda suka hada kin bayyana dan takarar da zai gaje shi a 2023 da kuma kin yin katsalandan ga sha’anin shari’ar Nnamdi Kanu.

Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta saki Nnamdi Kanu a yanzu ba, hasali ma yanzu ne yake da damar kare kansa game da suka da cin zarafi da ya dinga yi wa gwamnatin yayin da ya tsere zuwa Landan, bayan bada belinsa a 2017.

Gwamnatin ta Buhari na fama da suka kan yadda ake ganin abubuwa da dama sun tabarbare a mulkinsa duk da irin yakini da talakawa ke da shi a kansa.

Gwamnatin dai ta kara farashin man fetur, wanda kafin hawansa ya ce siyan man fetur din da tsada da ‘yan Najeriya ke yi wani zalunci ne.

Kayan masarufi sun yi mummunan tashin gwauron-zabi, lamarin da ya sake jefa miliyoyin mutane cikin kangin talauci, sai dai gwamnatin ta Buhari ta ce ta samar da hanyoyin ragewa talakawa radadi, wanda suka hadar da tsarin N-Power, tallafin COVID-19 da sauransu.

Matsalar tsaro musamman a yankin Arewancin kasar nan, wanda ’yan bindiga ke yi ba dare ba rana, inda suke garkuwa da mutane don karbar kudin fansa musamman a jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja, Sakkwato ya jefa dubban mutane cikin tsaka mai wuya.

Amma Buhari yayin hirar tasa ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar dakile mayakan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin kasar nan, inda kuma ya ce gwamnatinsa ta ayyana ’yan bindigar dajin a matsayin ’yan ta’adda.