✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai da na kusa kashe kaina saboda talauci – Tsohon dan kwallon Arsenal Eammnuel Eboue

Tsohon dan kwallon Arsenal Eammanuel Eboue ya bayyana irin halin taskun da ya tsinci kansa a ciki inda ya nuna saura kiris da ya kashe…

Tsohon dan kwallon Arsenal Eammanuel Eboue ya bayyana irin halin taskun da ya tsinci kansa a ciki inda ya nuna saura kiris da ya kashe kansa saboda tsakanin talauci.

Eboue, dan shekara 35 dan asalin Kwaddebuwa, ya buga wa kulob din Arsenal kwallo ne a tsawon shekaru bakwai kafin ya canza sheka zuwa kulob din Galatassaray na Turkiyya a shekarar 2011.

Yana daga cikin ’yan kwallon da suka buga wa Arsenal wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai (UEFA Champions League) a shekarar 2006 inda FC Barcelona ta doke su da ci 2-1.

Xan kwallon ya ce tun bayan da ya koma Turkiyya abubuwa suka rincabe masa bayan ya rabu da matarsa, bayan kotu ta umarci ta rike ’ya’yansu uku Clara mai shekara 14 da Maeba ’yar shekara 12 da karamin dansu da kuma daukacin kadarorin da ya mallaka.  Ya ce yanzu haka bai san inda tsohuwar matarsa da ’ya’yansa suke ba kuma tuni ya daina buga wa kulob din Galatassaray kwallo.

Xan kwallon ya ce al’amurra sun yi masa zafi inda ta kai a lokuta da dama yakan kulle kansa a daki ya kashe wuta don kada jami’an tsaro su kai masa farmaki tun da ya kasa biyan haraji na tsawon lokaci.  Hasalima sai da ta kai an kore shi a gidan da yake haya inda ya koma gidan wani abokinsa, inda abokin ya sauke shi a wani daki mai kama da gareji yana kwana a ciki.  Kuma shi yake yi wa abokin wanki da hannunsa da sauran harkokin gida yana biyansa dan abin da ba a rasa ba don ya tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum.

“A gaskiya na ga tasku a rayuwa don a wani lokaci na kan kalli kaina a madubi na yi tambayar wai shin da gaske ne na fada cikin wannan halin rayuwa na matsi?  A wani lokaci nakan ji kamar na kashe kaina don na huta,” inji Eboue.

Ebouye dai ya samu Miliyoyin kudi a lokacin da yake buga wa Arsenal kwallo amma rabuwar da ya yi da matarsa ce ta janyo masa fadawa cikin wannan matsala, bayan kotu ta umarci ya sadaukar da dukiyarsa da kuma ’ya’yansa ga matar.

Sai dai rahotanni sun nuna tuni kulob din Galatassaray na Turkiyya ya dauke shi aiki a matsayin kocin matasa don ya samu sakin gudanar da rayuwa.