✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai mun duba cancanta muke nadin mukamai — Buhari

Ana zargin gwamnatin Buhari da nuna wariya wajen nade-naden mukaman da take yi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce dukkanin nade-naden mukamai da gwamnatinsa ke yi na zuwa ne bisa la’akari da cancanta domin cimma muradun al’ummar kasar nan.

Hakan na zuwa ne yayin wata hira da Shugaban ya yi a safiyar Alhamis tare da Gidan Talabijin na Arise.

Wasu dai na sukar gwamnatin Shugaba Buhari da zargin cewa tana nuna wariya da son kai wajen nade-naden mukaman da take yi.

A bayan nan aka rika cece-kuce bayan nada Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya wanda ya maye gurbin marigayi Janar Ibrahim Attahiru da ajali ya katse masa hanzari yayin wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a watan jiya.

Sai dai yayin tattaunawar, Shugaba Buhari ya musanta zargin da cewa masu ikirarin hakan ba su madogara ta kwararan dalilai.

Ya bayyana cewa, “wadanda suka san yadda muke gudanar da gwamnatinmu, sun san cewa mun nada mutane da dama daga Kudu maso Gabashin a manyan mukamai.

“Muna la’akari da duk wata cancanta da ta shafi kwarewar mutum da sadaukarwa kafin mu yi nadin mukami.

“Idan har ana so a samu wanda zai jagoranci sojoji cikin tsari da inganci, dole ne a duba nagarta da kuma kwarewar mutum ta fuskar sanin makamar aikin.

“A halin da Najeriya ke ciki na fuskantar kalubalen tsaro daga kusan kowane yanki a fadin kasar, muna bukatar wanda yake da kwarewar fita filin daga.

“Mun sake sauya fasalin tsaro a kasar domin mu rubanya kokarin da muke yi wajen inganta tsaro a kasar.

“Muna da tabbacin cewa gwamnatinmu tana ci gaba da samun nasarori a dukkan ayyukan da ta sanya a gaba, sai dai ba muna yi ne don ganin ido ba, kuma hakan ya sanya ba ma yayata nasarorin da muke samu,” inji Buhari.