✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai mun ga bayan ta’addanci a Najeriya a 2021 —Buhari

2021 shekara ce ta aiki da daukar matakan kammala jan aikin

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce 2021 shekara ce ta yin aiki da daukar mataki kawar da ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Buhari ya ce akwai yiwuwar yin nasara nan ba jimawa ba a yakin da ake yi da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

“Bana shekara ce ta aiki, kuma za mu kammala abin da muka fara; Kwanan nan komai zai zama tarihi. Kawai a dage a ci gaba da yi mana addu’a,” inji shi.

Ya ce don haka ya zama tilas ’yan Najeriya su dage da addu’a muddin suna so a kawo karshen matsalar da ta shafe sama da shekara 11 tana addabar kasar.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi a yayin Sallar Juma’a da aka shirya domin bikin Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya ta bana a Abuja.

Ya kuma ce Najeriya ba za ta taba mantawa da ’yan Mazana Jiyan ba, musamman irin gudunmawar da suka bayar wajen kare martabar Najeriya.

Daga nan ya yi wa iyalan ’yan mazan jiyan alkawarin cewa gwamnati na sane da irin gudunmawarsu, kuma ba za ta taba bari su wulakanta ba.

Tun da farko sai da babban Limamin Masallacin Kasa, Dakta Mohammed Adam ya yi wa mamatan addu’a tare da rokon Allah Ya kawo karshen kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.