✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sakacin mahukunta ke haifar da yawan fasa gidajen yari’

Wani manomi a garin Oyo Ustaz Tahir Zubairu ya ce, “Sakaci daga bangaren mahukuntan kasa ne yake haifar da yawan fasa gidajen yari da mazauna…

Wani manomi a garin Oyo Ustaz Tahir Zubairu ya ce, “Sakaci daga bangaren mahukuntan kasa ne yake haifar da yawan fasa gidajen yari da mazauna ciki da aka killace su domin gyara halayensu suke samun damar tserewa.

“Idan akwai tsauraran matakan tsaro to zai yi wuyar gaske mahara ko ’yan bindiga su iya kusantar irin wadannan muhimman wurare,” inji shi.

Zubairu ya bayyana haka ne cikin zantawarsa da Aminiya jim kadan, bayan samun labarin harin da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai gidan yarin Abolongo da ke garin Oyo cikin daren Juma’a da ta gabata, inda suka bindige wani soja da jami’in Amotekun kafin su fasa gidan yarin da fursunoni 837 suka tsere.

Ya ce, “Duk da yake an gina wannan gidan yari ne a cikin daji nesa da gari, amma idan akwai tsauraran matakan tsaro to kuwa babu wanda zai iya kusantar wannan wuri da mummunan nufi.”

Manomin ya nuna takaicin yawan fasa gidajen yari na kasa a daidai lokacin da ake tsare da irin mutanen da suka aikata manyan laifuka.

Ya ce, daukar tsauraran matakan tsaro ne kadai zai yi maganin aukuwar irin wannan abun kunya a nan gaba.

Bayan mahara sun fasa gidan yarin na Abolongo cikin daren ranar Juma’a fursunoni 837 ne suka tsere cikin daren. Amma jami’an tsaron da suka bi sawun fursunonin sun yi nasarar kama 446 daga cikinsu. Kamar yadda mahukunta suka sanar.

Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola da Kwanturola-Janar na Hukumar Gidajen Yari Halliru Nababa da Kwamishinar ’Yan sanda Uwargida Ngozi Onadeko da Mai martaba Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi duka sun kai ziyarar gani da ido a lokuta daban-daban zuwa wannan gidan yari da aka gina cikin shekarar 2007.